Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 15:11:29    
Me ka sani game da tauraruwa mai wutsiya

cri

Lokacin da ake batu kan tauraruwa mai wutsiya, daga farko a cikin ran dan Adam, wata tauraruwa wadda take da wata doguwar wutsiya kuma take tafiya da sauri a cikin sararin sama. Yanzu, domin ilmi game da taurari yana yaduwa sosai, yawancin mutane sun san ainihin halin tauraruwa mai wutsiya daidai, kuma ana duba tautaruwa mai wutsiya ne bisa ilmin kimiyya. Amma a da, domin ba a san shi sosai ba, a nan kasar Sin ana ganin cewa, tauraruwa mai wutsiya tauraruwa ce da ke kawo wa dan Adam masifa. Sabo da haka, a nan kasar Sin ba a son taurarruwa mai wutsiya a da. Wasu Sinawa su kan kiran shi tauraruwa mai kawo masifa. Idan an gan shi yana tafiya a sararin sama, to, shi ke nan, za ta kai shi masifa. Domin tauraruwa mai wutsiya tana tafiya a sararin sama kamar yadda ake share daki da wata tsintsiya. Tun da haka, ana kuma kiranta tauraruwar tsintsiya wadda ke kawo mana masifa. Wasu mutanen kasar Sin suna jin tsoron ganinta a da.

A kan tarihi, ana ganin cewa, tauraruwa mai wutsiya bako ne da ya zo gidan rana amma ba a gayyace shi ba. Turawa ma ba su san tauraruwa mai wutsiya sosai ba. Tun daga lokacin da babban dan kimiyya Aristotle yake, a cikin shekaru dubbai, Turawa sun yi tsammani cewa, tauraruwa mai wutsiya ba tauraruwa ba ce sai an kunna wuta a sararin sama. Sabo da haka, dan kimiyya na kasar Poland Copernicus Nicholas wanda ya yi tsammani cewar rana cibiyar duniya ce, shi ma ya yi tsammani cewa, "tauraruwa mai wutsiya da mutanen Greek suke kira, iska ce da ke sararin sama." Har karshen karni na 16, bayan ya duba taurari, a karo na farko ne Tycho Brahe, wato wani dan kimiyya na Denmark ya tabbatar da cewa, babbar tauraruwa mai wutsiya da ta fito a shekarar 1577 ta fi wata nisa. A sakamakon haka, an fara sanin ainihin halin tauraruwa mai wutsiya. Daga baya, 'yan kimiyya da masu kishin ilmin tautari ba tare da kasala ba ne sun sami halin musamman iri-iri na tauraruwa mai wutsiya. An fara sanin tauraruwa mai wutsiya a hankali a hankali. Ya zuwa yanzu, an riga an ga taurari masu wutsiya fiye da 1600 bi da bi. Amma kowa ya sani, wadannan taurari masu wutsiya ba dukkan taurari masu wutsiya da ke tafiya a sararin sama ba sai kadan ne. Domin tauraruwa mai wutsiya ba ta da haske sosai, sai ya iso wurin da ke nisa da mu, za su iya ganinta, amma idan ya je wurin da ke kusa da rana, to, shi ke nan, ba za mu iya ganinta ba sam sam. An kiyasta cewa, a cikin gidan rana kawai, akwai taurari masu wutsiya fiye da miliyan 17, amma yawancinsu suna tafiya a wuraren da ke nisa da rana.

A cikin dukkan taurari masu wutsiya da aka sani, ko shakka babu wadda ta fi shahara ita ce tauraruwa mai wutsiya da ake kiranta tauraruwa mai wutsiya ta Halley. Wannan tauraruwar farko ce da aka kidaya aka tabbatar da cewa tana kasancewa a duniya. A karni na 17, dan kimiyya na kasar Ingila Edmund Halley ya kidaya hanyar wata tauraruwa mai wutsiya da ta taba fitowa a shekarar 1682. Bayan ya yi kidaya, ya sami sakamako cewa, hanyar da wannan tauraruwa mai wutsiya take bi tana daidai da hanyar da tauraruwa mai wutsiya da ta taba fitowa a shekarar 1607 da a shekarar 1531. Edmund Halley ya yi kidaya ya yi kidaya har sau da yawa kuma ya tabbatar da cewa, wannan sau uku ne wata tauraruwa mai wutsiya daya ta dawo ta iso idonmu. Har ya yi hasashen cewa kowane shekaru 76 ne wannan tauraruwa mai wutsiya tana dawowa idonmu, kuma a shekarar 1758 ko shekarar 1759 ce wannan tauraruwa mai wutsiya za ta sake fitowa. Kodayake Edmund Halley bai iya ganin dawowar wannan tauraruwa mai wutsiya da kansa ba domin ya rasu a shekarar 1742, amma kamar yadda ya kiyasta, wannan tauraruwa mai wutsiya ta dawo a shekarar 1759, sauran 'yan kimiyya sun ga wannan tauraruwa mai wutsiya. Sabo da haka, an kira ta tauraruwa mai wutsiya ta Halley domin tunawa da Edmund Halley.

A nan kasar Sin ma akwai tarihi game da wannan tauraruwa mai wutsiya ta Halley sosai. Yau da shekaru fiye da dubu 2 tun daga lokacin daular Chunqiu, kowane karon da ta dawo, an rubuta hanyar da ta bi a cikin littafin tarihi daidai.