Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-28 15:17:00    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya hukumar tsaro ta jihar Tibet ta daidaita matsaloli 3 na fashewar bamabamai bi da bi a shiyyar Chamdu ta jihar Tibet, kuma ta kama mutane 16 wadanda ake tuhumarsu da laifuffukan fashewar bamabamai, sakamakon haka an murkushe rukunin 'yan kawo baraka na Tibet sosai.

A ran 5 ga watan Afril da dare, wasu sufaye na dakin ibadan Odser na gundumar Mangkam sun jefa bom kan wata na'urar raba wutar lantarki. A ran 13 ga watan Mayu na wannan shekara kuma hukumar tsaro ta jihar Tibet ta kama mutane 5 da aka tuhume su ga yin wannan laifi.

Haka kuma a ran 7 da ran 15 ga watan Afril da dare, an barkata mugunta ta hanyar jefa bamabamai a sauran wurare 2 na jihar Tibet, daga baya kuma hukumar tsaro ta jihar ta wasu mutane da ake tuhumarsu ga yin wadannan miyagun laifuffuka, kuma har ila yau da akwai mutane 3 da ake tuhumarsu da laifi wadanda ba a kama su ba tukuna.

---- Kwanan baya, an rufe bikin rawa na kabilun kasashen duniya na karo na farko wanda aka shafe kwanaki 11 ana yin sa a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Ma'aikatar al'adu ta kasar Sin da gwamnatin jama'ar jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta su ne suka shirya wannan biki tare, suna fatan za a mai da rawa a matsayin gada don sa kaimi ga yin mu'amalar al'adu tsakanin Sin da kasashen waje, da kara dankon zumunci tsakanin Sin da sauran kasashe daban-daban, sa'an nan kuma domin bayyana fasahar jama'a ta jihar Xinjiang daga fannoni da yawa.

Da akwai kungiyoyin wasannin fasahar rawa 16 wadanda suka zo daga kasashe 10 cikin har da kasar Sin da Rasha da Masar da Indiya sun halarci wannan bikin rawa ta kabilun kasashen duniya, wadanda kuma suka nuna wasanni har sau 45 masu halaye daban-daban domin 'yan kallo.

Ban da wannan kuma, a gun bikin rawa, an shirya taron dandalin fadi albarkacin bakinka kan ilmin raye-raye, da yin nunin kayayyakin tarihi masu daraja na jihar Xijiang, da kuma nunin sakamakon da aka samu wajen kiyaye abubuwan al'adun tarihi da aka gada daga kakanni zuwa kakanni.(Umaru)