Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-28 15:15:50    
Bayani kan halin da ake ciki a jihar Tibet wajen bunkasa al'adun jama'a

cri

Jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin wata jiha ce ta kananan kabilu wadda take da al'adun jama'a da yawa. Kafin shekaru 50 da suka wuce, wato a lokacin da ake tafiyar da tsarin bayi manoma na gargajiya wanda yake haduwar siyasa da addini a jihar, an mai da al'adun addini a muhimmin matsayi, kuma ba a yi gadon al'adun jama'a ba sabo da rishin kulawar da aka nuna musu. Daga karshen shekaru na 50 na karnin da ya wuce, gwamnatin kasar Sin ta kara rubanyan kokari don ba da kariya ga al'adun jama'a na jihar Tibet, sabo da haka an farfado da al'adun jama'a yadda ya kamata. Jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu kai ku ziyara jihar Tibet domin ganin yadda ake bunkasa al'adun jama'a a can.

Mr. Tsering Phuntsok, mataimakin shugaban ofishin binciken ilmin kabilu na cibiyar binciken kimiyya ta zaman al'umma ta Jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa,

"Kasarmu tana ba da muhimmanci sosai ga abubuwan al'adun tarihi da aka gada daga kakanni zuwa kakanni, ciki har da aikin shiryawa da bugawa da yin binciken babban littafin wake-wake mai suna "Tarihin sarkin Gasar", an mai da wannan aiki a matsayin muhimmin aikin binciken kimiyyar zaman al'umma na kasar Sin."


1 2 3