Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-24 18:05:10    
Birnin Beijing yana kokarin tabbatar da zirga-zirga domin gasar wasannin Olympic

cri

Tun daga kwanan baya da suka gabata, an fara aiwatar da manufofin tabbatar da zirga-zirgar gasar wasannin Olympic ta Beijing, ciki har da manufar kayyade zirga-zirgar motoci a birnin Beijing. Hukumar sa ido kan babbar zirga-zirgar jama'a ta Beijint ta yi hasashen cewa, lokacin da ake aiwatar da manufar kayyade zirga-zirgar motoci, yawan karin mutanen da za su dauki kayayyakin ababen hawa zai kai fiye da miliyan 4 a kowace rana. Sabo da haka, birnin Beijing ya riga ya dauki matakai iri iri domin kara karfin babbar zirga-zirgar jama'a.

Tun daga ran 20 ga watan Yuli ne, aka soma aiwatar da manufar kayyade zirga-zirgar motoci bisa lambobinsu. Kafin a kaddamar da wannan manufa, a ran 19 ga wata da yamma, a lokaci daya ne aka kaddamar da hanyoyin jirgin kasa da ke tafiya a karkashin kasa guda 3 domin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Mr. Zhou Zhengyu, mataimakin shugaban kwamitin kula da zirga-zirgar birnin Beijing ya ce, bayan kaddamar da wadannan hanyoyin jirgin kasa guda 3, yawan hanyoyin jirgin kasa da ke tafiya a karkashin kasa ya kai 8, tsawonsu ya kai kilomita metan.

Mr. Mamoun Saada, wakilin gidan talibijin na Aljazeera da ke nan kasar Sin ya yi shekaru 3 yana aiki a Beijing. Yana farin ciki sosai domin kaddamar da wata hanyar jirgin kasa da ke tafiya a karkashin kasa wadda aka shimfida domin gasar wasannin Olympic ta Beijing musamman. Mr. Mamoun ya ce, "Wannan hanya tana da ma'ana sosai. Tasoshinta hudu suna almantar da lokuta hudu na kowace shekara. A waje daya kuma, ana daukar jirgin kasa a wannan hanya cikin sauki da kwanciyar hankali. Tun daga unguwar 'yan jaridu da cibiyar watsa labaru ta rediyo ta kasa da kasa da babbar cibiyar watsa labaru da aka gina domin gasar wasannin Olympic ta Beijing, dukkan 'yan jaridu za su ji saukin daukar jiragen kasa a kan wannan hanya."

An yi hasashen cewa, wadannan hanyoyin jiragen kasa da ke tafiya a karkashin kasa za su dauki fasinjoji fiye da miliyan 1 a kowace rana. Sabo da haka, dukkan hanyoyin jiragen kasa da ke tafiya a karkashin kasa na Beijing za su iya daukar mutane miliyan 5 a kowace rana.

Ban da hanyoyin jiragen kasa da ke tafiya a karkashin kasa, birnin Beijing ya dauki sauran matakai iri daban daban, kamar ya sayi sabbin kayayyakin ababen hawa, kuma ya tsawaita lokacin aikin kayayyakin ababen hawa domin kyautata ingancin sufurin jama'a. An yi hasashen cewa, yawan karin mutanen da kayayyakin ababen hawa za su iya dauka a lokacin gasar wasannin Olympic zai kai fiye da miliyan 2 da dudu dari 8 a kowace rana.

1 2