Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-17 15:38:05    
Hu Jintao ya yi gaisuwa ga wakilan 'yan firamare da sakandare da za su je kasar Rasha don samun jiyya

cri

Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar kuma shugaban kwamitin rundunar soja na kasar Sin Hu Jintao ya yi gaisuwa ga wakilan daliban firamare da sakandare na yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa wadanda za su je kasar Rasha don samun jiyya a ran 16 ga wata a Zhongnanhai.

Bisa gayyatar da gwamnatin Rasha ta yi, daliban firamare da sakandare dubu daya na yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa za su samu hidimomi jiyya daga ran 17 ga watan Yuli zuwa ran 5 ga watan Agusta a wurare daban daban na kasar Rasha. Kafin su tashi, Hu Jintao ya gayyaci wadannan yara zuwa Zhongnanhai. A yayin da yake hira da yaran, a madadin jam'iyyar kwaminis ta Sin da kuma gwamnatin kasar, Hu Jintao ya nuna jejeto ga wadannan yara sosai, ya kuma kalubalanci da su jure wahalhalu don raya kasa mahaifa. Kazalika, Hu Jintao yana fatan yaran za su ci gajiyar hidimomin jiyya da kara musanyar ra'ayi da yaran kasar Rasha don zama wakilan sada zumunta tsakanin kasashen biyu.(Lami)