Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 15:30:19    
Titin Wangfujing na jiran matafiya na gida da na waje

cri

A cibiyar birnin Beijing, akwai wani titi da ya shahara saboda harkokin kasuwanci, kuma an kebe shi domin tafiya a kasa, sunansa shi ne titin Wangfujing, ana kiransa titin Jinjie, wato titi mai kawo zinariya. A kan wannan titi mai tsawon mita kusan dubu 2, ana sayar da kayayyaki iri daban daban. Matafiya su kan yi saye-saye da nishadi a wannan titi.

Titin Wangfujing na kasancewa cibiyar birnin Beijing, yana kuma gabashin babban filin Tian'anmen. In kun shiga jirgin kasa mai lamba 1 da ke karkashin kasa, to, za ku isa titin a daidai tashar Wangfujing. A shekarar 1903, titin Wangfujing ya zama wani titin kasuwanci. A lokacin can, a kusa da titin, akwai ofisoshin jakadanci na kasashen waje da yawa, shi ya sa wasu kantuna da bankunan da ke ba da hidima ga mutanen waje suka soma bude kofa a titin Wangfujing, sannu a hankali wani titin kasuwanci na zamani ya bullo.

Bayan shekaru 1950, titinWangfujing ya zama yankin kasuwanci mai wadata da kasuwar Dong'an da babban ginin sayarwa na Wangfujing suka zama babban bangarensa. A sakamakon bunkasuwa mai tsawon shekaru, yanzu titin Wangfujing ya zama wurin yin saye-saye da nishadi na zamani. Baya ga wasu shahararrun tambarorin duniya, an fi samun kantuna masu tsawon darurukan shekaru a titin Wangfujing, in an kwatanta shi da sauran wuraren kasar Sin.


1 2 3 4