
Bugu da kari kuma manazarta sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba a san mene ne dalilin da ya sa yin motsa jiki ke iya rage yiyuwar kamuwa da ciwon sankarar huhu ba. Amma ana ganin cewa, mai yiyuwa ne sabo da yin motsa jiki yana iya kyautata aikin huhu, ta haka za a iya rage yawan kwayoyin sankara da ke cikin huhu.
Kwararre na farko a fannin kiwon lafiya na kungiyar kula da huhu ta kasar Amurka Norman Edelman ya bayyana cewa, yiyuwar kamuwa da ciwon sankarar huhu ga masu shan taba ta ninka sau 10 idan an kwatanta da marasa shan taba, shi ya sa bai kamata masu shan taba su dogara bisa yin motsa jiki wajen rage hadarin kamuwa da ciwon sankarar huhu ba.(Kande Gao) 1 2 3
|