Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-10 18:02:02    
Garin Bayinhaote da ke jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin

cri

Birnin Beijing shi ne hedkwatar kasar Sin. Akwai shahararrun wuraren tarihi na al'adu da yawa a wannan birni, kamar Babbar Ganuwa, wato Great Wall da fadar sarakuna, wato Forbidden City. To, masu sauraro, ko kun san cewa, a jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin da ke da nisan kilomita misalin dubu daya tsakaninta da Beijing a arewa maso yamma, akwai wani wuri da ake kiran shi karamar Beijing.

Garin Bayinhaote da ke jihar Mongolia ta Gida ake kiran shi 'karamar Beijing' a tarihi. A bakin 'yan kabilar Mongolia, ma'anar Bayinhaote shi ne gari mai wadata. Bayinhaote wani gari ne da ke kuryar yamma a jihar Mongolia ta Gida. Ko da yake yankin Alashan yana da girma, amma hamada ta mamaye yawancinsa. Bayinhaote ita ce zango a cikin wannan hamada. Ko da yake wannan gari ba ya da girma, amma ya iya nuna halin musamman irin na gargajiya.

Yau da shekaru 280 ko fiye da suka wuce, an taba ta da tawaye a lardin Qinghai da ke arewa mao yammacin kasar Sin, 'yan sarki na kabilar Mongolia da suka zo daga Mongolia ta Gida sun kwantar da tawaye bisa umurnin da aka ba su, sun ba da gudummowa mai muhimmanci. Shi ya sa mahukuntan lokacin can sun tsai da kudurin gina wata daula a matsayin abun kyauta, wato Bayinhaote a yanzu.

Bayan kafuwar Bayinhaote, dattijai da yawa sun kaura zuwa nan, sannu a hankali sun zama wani babban iyalin masarauta. Sun gina manyan gidaje da gidajen ibada, wadanda tsare-tsarensu da girmansu suka yi kama da fadar da aka samu a Beijing. Sa'an nan kuma, fararen hula su kan gina gidajensu bisa tsarin gidajen kwana masu fasali hudu irin na da na Beijing a lokacin can. Shi ya sa aka fara kira Bayinhaote karamar Beijing da ke waje da Babbar Ganuwa. Wang Jianping, wani jami'in hukumar kula da ayyukan gine-gine a birane ta yankin Alashan, inda Bayinhaote take ciki, ya bayyana cewa,'Don me ake kiran Bayinhaote karamar Beijing? Dalilin shi ne domin Bayinhaote tana karkashin shugabancin mahukuntan Beijing na lokacin can kai tsaye, kuma gine-ginenta da tsare-tsaren birni da kuma shirye-shiryen da ta tsara wajen raya birni sun yi kama da salon da aka bi wajen raya Beijing. '

An ce, an gina gine-gine da lambuna masu halin musamman irin na lambun shakatawa na sarakuna na Beijing a Bayinhaote, amma yanzu sun zama wuraren nishadi na fararen hula.

Ko da yake garin Bayinhaote yana da shekaru 280 ko fiye da kafuwa, amma saboda yana kasancewa yankunan karkara a hamada, shi ya sa kafin kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, shi ne wani karamin gari mai fadin misalin murabba'in kilomita dubu 30 kawai. A can da, an bude wasu kananan shaguna kawai a duk garin Bayinhaote, amma yanzu fadin garin ya kai misalin murabba'in kilomita dubu 80, akwai makarantu iri daban daban kusan guda 50, yawan mazauna ya kai kusan dubu 150. Haka kuma, an fito da tsarin hanyoyin mota a wannan gari, inda motoci da busukur ke zirga-zirga a kai. A waje daya kuma, na'urorin aikin sadarwa sun hada garin Bayinhaote da sauran wuraren duniya tare, ta haka, wannan garin da ke waje da Babbar Ganuwa ya taka kan hanyar raya kansa na zamani.

A tsohon bangaren garin Bayinhaote, akwai kantuna da shaguna da yawa, mutane su kan cika kasuwanni, musamman ma kantunan sayar da lu'ulu'u irin na Alashan. Sa'an nan kuma, a sabon bangaren garin, wata hanyar mota mai fadi ta ratsa garin ta isa kafar babban tsaunin Helanshan. A gefunan hanyar, an gina manyan gidaje. Abin da ya fi jawo hankali shi ne mutum-mutumin farin rakumi da ke gabashin garin, yanzu ya riga ya zama alamar wannan gari na Bayinhaote.

Mai yiwuwa ne wasu za su yi tambayar cewa, a kan fama da fari da karancin ruwan sama a hamada a duk shekara, kuma iska kan buga da karfi, amma an sami itatuwa da furanni masu tarin yawa a garin Bayinhaote. Yana kasancewa da babban bambanci a tsakanin garin Bayinhaote da sauran wurare a wannan hamada. Mr. Wang ya gaya mana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin hukumar wurin tana dora muhimmanci sosai kan kiyaye muhalli. Ya ce,'Sarakuna na zamanin dauloli daban daban sun dora muhimmanci sosai kan kiyaye muhallin Bayinhaote. A lokacin can, sun tsara tsauraran ka'idoji kan debo ruwa da yin amfani da gonaki, sun hana gina gidaje yadda aka ga dama. Bayan kafuwa sabuwar kasar Sin, hukumar wurin ta ci gaba da raya garin bisa tsarin da aka tsara a da, tana mai da hankali kan dasa itatuwa da ciyayi. A ko wace shekara ta kan zuba kudade da yawa kan dasa itatuwa da ciyayi yadda ya kamata a wannan gari.'