Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-10 17:51:00    
Labarai guda biyu kan mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu cigaba da sanya muku labarai guda biyu da wakilin gidan rediyon CRI ya rubuto mana a kan mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Wadannan labarai biyu na shafar 'yan mata guda biyu, wadanda aka haife su bayan shekarar 1980 amma kafin shekarar 1990.

Qi Mingyu, yarinya ce wadda aka haife ta a shekara ta 1982 a jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta dake arewacin kasar Sin. Ta koyi aikin ilmantarwa a fannin wasannin motsa jiki a cikin jami'a. Bayan aukuwar mummunan bala'in girgizar kasa, Qi Mingyu ta kuduri aniyar zama wata mai aikin sa-kai a yankin dake fama da bala'in. Ta hanyar sadarwa ta Internet ne, Qi ta kulla zumunci tare da sauran samari 5 wadanda suna rukunin shekaru guda. Sun sayi wasu injuna da kayayyakin yaki da bala'in girgizar kasa da yin ceto, daga bisani ne, sun je yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su.

"An haife ni a shekarar 1982, labarin aukuwar mummunan bala'in girgizar kasa ya burge ni kwarai da gaske. A wancan lokaci, ina so in taimaki wadanda ke fama da bala'in, na san akwai mutane da dama wadanda suka sadaukar da jininsu da bayar da kudaden taimako. Baya ga wadannan abubuwa biyu, ina so in yi sauran abubuwa domin bayar musu taimako, shi ya sa na yanke shawarar tafiya zuwa yankin dake fama da bala'in girgizar kasa domin ganema idona kan halin da ake ciki a wurin. A matsayin wata yarinya wadda aka haife ni bayan shekarar 1980, kuma na taba koyon aikin ilmantarwa a fannin wasannin motsa jiki, saboda haka ne ina cike da karfi da kuzari wajen ceto mutane. A kan hanyarmu zuwa yankin dake fama da bala'in girgizar kasa, ni da abokanmu mun ce, ya kamata mu samari wadanda aka haife mu bayan shekarar 1980 mu bayar da taimako ga dukkan zamantakewar al'umma, mu taka rawar a-zo-a-gani ga wadanda aka haife su bayan shekarar 1990."

Domin kada su kara samar da matsaloli ga mutanen da bala'in girgizar ya shafa, wadannan samari guda shida sun shirya ruwan sha, da abinci, da magunguna, da tantuna, da kayayyakin sutura da kansu. Yayin take zantawa kan wannan karamar kungiyar dake kunshe da samari shida, Qi Mingyu ta yi murmushi tana cewa: "Kungiyarmu na da injuna da kayayyaki namu. Ban da wadannan kuma, muna da wani dakaren da ya yi ritaya daga aikin soja, da wasu kyawawan likitoci, da samari biyu wadanda suka gama karatunsu a jami'a. Dukkaninmu muna cike da karfi da zafin nama domin bayar da taimako ga mutanen da suke fama da bala'in girgizar kasa."

Wannan karamar kungiyar dake dauke da samari guda shida wadanda aka haife su bayan shekarar 1980 ta yi aiki tukuru har na tsawon kwanaki 9 a yankuna daban-daban da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su a lardin Sichuan, ciki har da Jiangyou, da garin Longmenshan, da tafkin da ya samo asali daga bala'in girgizar kasa da ya yi a Tanjiashan, da birnin Dujiangyan da dai sauransu. Sun yi aikin kwashe mutanen da suka yi cincirindo a tafkin da ya samo asali daga bala'in girgizar kasa, da rarraba kayayyakin agaji ga mutane.

"Na ji an ce, an yi hadari sosai a tafkin da ta samo asali daga bala'in girgizar kasa da ya yi a yankin Tangjiashan, shi ya sa an ba mu aikin kwashe mutanen da suka yi cincirindo a wurin. Da farko dai, akwai wasu mutane wadanda ba su so su bar wurin. Domin warware wannan matsala, mun yi hira tare da su, a karshe dai dukkan mutane sun yi kaura daga wurin. A wajen daya kuma, mun je wata kasuwa a birnin Chengdu mun sayi wasu abubuwan yau da kullum, ciki har da kayan lambu, da madara, da kayayyakin jarirai, mun tura su zuwa yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa."

Yayin da take zantawa kan abubuwan da ta samu daga aikin yaki da bala'in girgizar kasa da yin ceto har na tsawon kwanaki 9, Qi Mingyu ta ce, a lokacin da, ta fi son yin wasa, ba ta san yadda za ta yi domin kulawa da iyayenta ba. Amma a lokacin da take yankin dake fama da bala'in girgizar kasa a cikin kwanaki kalilan, Qi ta yi girma sosai, ta san yadda za ta yi domin darajanta kauna da tausayin dake kasancewa a tsakanin mutane. Yayin da wakilinmu ya tambaye ta ko za ta sake zuwa wurin, ba tare da wata-wata ba ta ce: "Ina so in sake zuwa wurin! Na yi aiki karami ne a wannan karo, shi ya sa ina so in sake zuwa wurin domin gudanar da ayyukan tsugunar da mutane da sake farfado da yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa. Na ji labari cewa, ana bukatar karin masu aikin ceto."

Kamar yarinya Qi Mingyu take, 'yar lardin Sichuan wadda a yanzu haka take aiki a birnin Shanghai, Cai Cai, ita ma aka haife ta bayan shekarar 1980 amma kafin shekarar 1990. Ta zama wata mai aikin sa-kai ba tare da wani jinkiri ba bayan aukuwar bala'in girgizar kasa.

"An haife ni a ranar 5 ga watan Maris na shekara ta 1983, na fito daga birnin Deyang na lardin Sichuan. Bayan da na samu labarin faruwar mummunan bala'in girgizar kasa a garinmu, na nuna damuwa sosai. Ba tare da bata lokaci ba na sayi tikitin jirgin sama na koma gida. Da na isa gidana, na yi mamaki kwarai da gaske, saboda na ga gidaje sun ruguje, ko'ina akwai baraguzan gine-gine. Bayan da na daidaita harkokin gidana, ban zame ko'ina ba sai dakin wasan motsa jiki na Jiuzhou dake birnin Mianyang, inda na gudanar da ayyukan rarraba magunguna, da kananan littattafai kan yadda za'a yi domin riga-kafin yaduwar cututtuka. Akwai wasu mutanen waje a wurin, kuma na taba koyon harshen waje, shi ya sa na zama wata tafinta gare su, domin rarraba wasu 'yan tsana ga kananan yara dake tantuna."

Cai Cai ta gano cewa, da ita da mutane da dama wadanda suka yi aikin sa-kai a dakin wasan motsa jiki na Jiuzhou suna rukunin shekaru guda. Ko da yake akasarinsu samari ne, amma sun gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

"Galibinsu suna cikin shekara ta biyu suna jami'a, shekarunsa ya kai 20 da haihuwa kawai. Akasarinsu sun gudanar da aikin rarraba kananan littattafai da abinci. A wancan lokaci, yawan mutanen da suka zama a dakin wasan motsa jiki na Jiuzhou ya zarce dubu 20, cin abinci ya zama wata babbar matsala. Wadannan masu aikin sa-kai sun yi aikin tsabtace dakin, da yin riga-kafin yaduwar cututtuka, da rarraba magunguna, da gayawa mutane ina ne suka iya yin wanka. Saboda akwai mutane masu tarin yawa a wurin, shi ya sa wadannan masu aikin sa-kai sun taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye doka da oda."

A halin yanzu, Cai Cai ta riga ta koma wurin aikinta a birnin Shanghai. Ta ce, mummunan bala'in girgizar kasa da ya auku a wannan gami, ya kara mata sani kan nauyin dake bisa wuyan wadannan mutane wadanda aka haife su bayan shekarar 1980 amma kafin shekarar 1990.

"Bayan aukuwar bala'in girgizar kasa, na san kamata ya yi mu yi aiki tukuru domin sauke nauyin dake bisa wuyanmu ga dukkan zamantakewar al'umma. Tuni na yi aiki a wurin dake da nisa sosai da gidana, ban yi mu'amala da tuntuba sosai da gidana ba. Bayan faruwar bala'in girgizar kasa, na kara kulawa da harkokin gidana, da kara tuntuba da iyayena. A waje daya kuma, yanzu ina tafiyar da aikin cinikayya tsakanin kasa da kasa, kuma na sami zarafi da yawa wajen yin cudanya tare da kasashen ketare. Kamata ya yi in kiyaye kwarjinin kasar Sin a duniya yayin da nike aiki yau da kullum."

To, jama'a masu sauraro, kun dai saurari labarai biyu dangane da 'yan mata guda biyu wadanda aka haife su bayan shekarar 1980 amma kafin shekarar 1990 a nan kasar Sin. A lokacin da, ana tsammani samarin da aka haife su bayan shekarar 1980 amma kafin shekarar 1990, mutane ne da ba su sauke nauyin dake bisa wuyansu yadda ya kamata ba. Amma daga labaran da muka bayar a cikin shirinmu na yau, muna ganin cewa, wadannan samari sun yi ta girma sannu a hankali. Bayan da mummunan bala'in girgizar kasa ya fadawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, wadannan samari sun bayar da babban taimako da agaji ga aikin yaki da bala'in girgizar kasa da yin ceto