Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-08 17:01:49    
An fara koyar da wasan Peking Opera a makarantun firamare da sakandare na birnin Tianjin

cri

Liu Lianqun, wani kwarare na wasannin kwaikwayo na waka na birnin Tianjin ya bayyana cewa, yanzu dimbin kasashe sun shigad da al'adun da ke da halayen musamman na kabilu cikin ilmi na matakin farko. Bisa wannan matsayi, shigad da wasan Peking Opera cikin darussa zai ba da taimako wajen gadon al'adun kabilu. Kuma ya kara da cewa, "Mene ne nufin shigad da wasan Peking Opera cikin darussa? A ganina nufinsa shi ne horar da matasa daga makarantun firamare da sakandare domin su girmama da kuma lura da nagartattun al'adun kalibunsu, da kuma fahimtar fasahohin gargajiya na-gari namu, ta yadda za a iya yada al'adun kabilunmu daga zuriya zuwa zuriya, da kuma inganta karfin kasarmu na al'adu."

A idon Feng Jicai, sanannen marubuci kuma shugaban kawancen adabi da fasahohi na birnin Tianjin, shigad da wasan Peking Opera cikin darussan makarantun firamare da sakandare wani kyakkyawan mataki ne, amma a waje daya kuma ya ba da shawarar cewa, ban da wasan, ya kamata wurare daban daban na kasar Sin su kiyaye fasahohinsu na musamman domin shigad da dimbin fasahohin kabilu cikin darussa. (Kande Gao)


1 2