Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-07 15:23:36    
An sake samu fashewar bom na kunar bakin wake a babban birnin kasar Pakistan

cri

A ran 6 ga wata a birnin Islamabad, babban birnin kasar Pakistan, an samu wata fashewar bam na kunar bakin wake, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 10, yawancin mutanen da suka mutu su ne 'yan sanda, tare da sauran mutane fiye da 40 suka ji rauni. An tada fashewar bam ne a wurin da ke dab da masallacin 'Lal Masjid' da ya jawo hankulan duniya a da, mutane da yawa sun yi tarurruka a wajen masallacin 'Lal Masjid', domin tunawa da ranar cikon shekara daya da faruwar lamarin 'Lal Masjid'.

Shugaban kasar Pakistan Mr. Pervez Musharraf da kuma firayin ministan kasar Mr. Yousuf Raza Gilani sun kai suka sosai ga wannan lamarin fashewar bom. Mr. Musharraf ya sake jaddada cewa, gwamnatin kasar Pakistan za ta ci gaba da yaki da ta'addanci ba tare da kasala ba, Mr. Gilani ya ba da umurni ga ma'aikatar harkokin gida ta kasar Pakistan da ta binciki wannan lamari sarai.


1 2