Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-07 14:19:48    
Wata yarinya 'yar kabilar Han ta ba da kodarta kyauta ga wani yaro dan kabilar Uighur ta kasar Sin

cri

Kasar Sin wani babban iyali ne da ke hade da kabilu 56, mutane 'yan kabilu daban-daban suna kaunar juna da taimakawa junansu, yayin da bala'i ya faru, ba shakka dukkansu za su ba da karfinsu domin kau da bala'in. To, cikin shirinmu na yau, za mu ba ku wani labari mai sosa zuciya dangane da wata yarinya 'yar kabilar Han mai suna Wang Yanna ta ba da kodarta kyauta ga wani yaro dan kabilar Uighur mai suna Mao Lan Umair wanda kuma ke fama da ciwon fitsari.

Budurwa Wang Yanna wadda take da shekaru 23 da haihuwa wadda kuma ba ta yi zaman wadata ba, ta taba sayar da kayan ado da tufafi cikin kasuwanni, dukkan kudin shiga da ta samu a kowane wata ta ba da su ne ga uwarta domin agaza wa iyalinta wajen zaman yau da kullum. Wata rana cikin watan Satumba na shekarar da ta wuce, Budurwa Wang Yanna ta ga wani labari cikin jarida cewa, wani saurayi dan kabilar Uighur mai suna Maolan Umair ya kamu da ciwon fitsari, sabo da haka ta damu kwarai ta ce,

"Na ga labarin a jarida cewa, lambar jininsa B ne, ni ma haka ne, shi ya sa ina son yin jarrabawa. Ina gani cewa, bisa matsayina wata budurwa ta sabon zamani, ya kamata na yi tunani domin sauran mutane wato na ba da babban taimako ga wadanda suke bukata. Kome dabarar da ka dauka, in ka yi, ba za ka ji kunya ba."

Saurayi Maolan Umair yana da shekaru 18 da haihuwa, tsayin jikinsa ya kai mita 1.8, yana sha'awar wasannin motsa jiki musamman ma wasan kwallon kwando, amma abin bakin ciki shi ne a watan Maris na shekarar 2007, ba zato ba tsammani ya kamu da ciwon fitsari, ba yadda za a yi domin warkar da ciwonsa sai ta hanyar canja kodarsa. A ran 17 ga watan Satumba na shekarar da ta wuce, wata budurwa 'yar kabilar Han ta je wajen asibitin da saurayin ke kwance kuma tana son ta ba shi kodarta ba tare da neman biyan kamasho ba. Lalle wannan ya ba iyayen Maolan Umair mamaki kuma ya faranta musu rai kwarai da gaske.

Budurwa Wang Yanna ta gaya wa wakilinmu cikin kwanciyar hankali cewa,

"Dalilin da ya sa na yi haka ba don kome ba ila domin taimake shi ne kawai. Ina fatan zai yi girma lami lafiya, kuma zai iya yin zama da karatu lami lafiya. Sabo da haka na tsai da kuduri ga yin haka duk domin ci gaba da samun rayuwarsa a duniya."

Da ganin diyarsa ta tsaya haikan kan kudurin da ta tsayar, ubanta Mr. Wang Xiujiang shi ma ba zai hana ta yin haka ba. A ran 27 ga watan Maris na shekarar da muke ciki, an yi fida lami lafiya, kuma an samu babbar nasara daga dukkan fannoni. Uban budurwa da na saurayi sun dan doke wa junansu a kafada cewa, "Nan gaba, dukkan wadannan yara 2 naka ne kuma nawa ne, kuma dukkanmu iyali daya ne!" Mr. Liu Jian, darektan sashen warkar da ciwon koda na asibiti na farko na jami'ar koyon ilmin likitanci ta jihar Xinjiang ta kasar Sin ya ji dadi cewa,

"Ya kamata a ce wannan karo na farko ke nan da aka yi irin wannan fidar dashen gabobin jikin mutane tsakanin 'yan kabilu daban-daban wato tsakanin kabilar Han da ta Uighur. A galibi dai, yawan mutanen da aka samu domin yin wannan fidar dasa koda tsakanin mutane da ba na dangi ba ya kai kashi daya bisa dubu 100 kawai."

A rana ta 4 ta bayan fidar, budurwa Wang Yanna ta je ganawa da saurayi Maolan Umair cikin asibiti, ta ga fuskarsa na cike da annuri, sai ta kwantar da hankalinta, kuma ta yi farin ciki sabo da burinta ya cika.

Yanzu, budurwa Wang Yanna da saurayi Maolan Umair sun riga sun fita daga asibiti, kowanesu yana hutawa cikin gidansa na kansa, sun yi tamkar ya da kane, kuma sukan yi wa junansu gaishe-gaishe ta wayar tarho.