Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-07 10:50:54    
An samu farfado da muhimman ababen biyan bukatun jama'ar yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su a lardin Sichuan

cri

Yanzu haka a yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa a lardin Sichuan na kasar Sin, an samu farfado da muhimman ababen biyan bukatun jama'a, ciki har da ayyukan samar da ruwa, da hanyoyin mota, da ayyukan wutar lantarki, tare kuma da ayyukan sadarwa.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, ta hanyar gyarawa da sake farfado da manyan ayyukan samar da ruwa a daukacin kauyuka da garuruwan lardin Sichuan ne, mutanen da adadinsu ya tasam ma miliyan 6 sun sami ruwan sha. Kazalika kuma, an riga an kafa ayyukan samar da ruwa a matsugunai sama da 500, inda mutanen da yawansu ya tasam ma dubu 600 suka sami ruwan sha ba tare da matsala ba.

Bisa labarin da muka samu, an ce, tsarin zirga-zirgar hanyoyin mota na lardin Sichuan yana aiki yadda ya kamata, gaba daya dai yawan kauyuka da garuruwa wadanda suka sake samun wutar lantarki a lardin Sichuan ya kai 242, wanda ya dauki kashi 99 daga cikin dari na dukkan kauyuka da garuruwa wadanda aka katse musu wutar lantarki a sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa. A waje daya kuma, yawan kauyukan da aka sake farfado da ayyukan sadarwa ya zarce kashi 96 bisa dari.(Murtala)