Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-04 21:30:27    
Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta ce, ya kamata a kafa makarantu da asibitoci mafi inganci a yankunan girgizar kasa

cri

A ran 4 ga wata, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da ra'ayi kan gudanar da ayyukan sake gina gidaje bayan girgizar kasa a gundumar Wenchuan, inda aka bayyana cewa, ya kamata a maido da manyan ayyuka da suka shafi zaman rayuwar jama'a da ba da hidima ga jama'a da farko a yankunan girgizar kasa na gundumar Wenchuan, da kafa makarantu da asibitoci da dai sauran manyan ayyukan jama'a a matsayin gine gine mafi inganci, wadanda kuma jama'a suka fi kwantar da hankula kan su.

Ra'ayin ya ce, kasar Sin za ta yi kokari sosai domin kammala aikin sake gina gidaje bayan girgizar kasa a cikin shekaru 3 masu zuwa, ta yadda zaman rayuwar jama'a da yanayin aikin kawo albarka za su kai matsayinsu kafin girgizar kasa har ma su wuce, domin samar da wani kyakkyawan tushe wajen samun bunkasuwa cikin dogon lokaci.(Danladi)