Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-03 17:04:07    
Dalibai biyu da malama guda yana daya

cri

Lin Hao, dalibi ne mai shekaru 9 da rabi da haihuwa na makarantar firamare ta Yuzixi ta garin Yingxiu na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. A lokacin da mummunan bala'in girgizar kasa ya faru, an binne Lin Hao da daliban ajinsa a karkashin baraguzan gine-gine, ciki har da manyan duwatsu masu nauyin gaske wadanda suka fado kasa, ko motsi kuma bai iya yi ba. Bayan da aka binne shi har na tsawon awoyi biyu, Lin Hao ya fara yunkurinsa na rarrafe zuwa waje. Sakamakon kokari ba tare da kasala ba da ya yi, wannan yaro wanda siriri ne sosai kuma mai karamin jiki ya fita waje cikin nasara a karshe! Amma a daidai wannan lokaci, Lin Hao bai tsere daga wannan wuri ba, ya dukufa ka'in da na'in wajen ceto sauran abokan arzikinsa guda biyu, wadanda aka binne su cikin tarkacen gine-ginen da wasu abubuwa suka yiwa kaca-kaca.

"Akwai abokan karatuna biyu wadanda suka danna ni. Na yi iyakacin kokarin kurda ta baraguzan gine-gine na fita, daga baya ne, na fito da abokan karatuna wadanda suka riga suka suma. Sa'annan na mika su zuwa ga shugaban makarantarmu, daga bisani kuma, mamansu sun isa wurin sun dauki yaransu zuwa gida."

Lin Hao yana da abokan karatu 30 a cikin aji guda, amma akwai dalibai sama da 10 daga cikinsu kawai wadanda suka tsallake rijiya da baya, ciki har da wadannan dalibai biyu da Lin Hao ya ceto. Yayin da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya koma wurin domin ceton abokan karatunsa bayan da ya fita daga baraguzan gine-gine, amsarsa na takaitacciya ce sosai. Ya ce:

"Saboda ni shugaban ajinmu ne!"

Domin kokarin ceton abokan karatunsa, Lin Hao ya ji raunuka a kansa. Yayin da manema labaru suka kai masa ziyara don jin ta bakinsa, ya bayyana cikin nitsuwa cewar:

"Tuni dai ban ji rauni ba, na samu rauni ne yayin da nike kokarin fito da su daga tarkacen gine-gine."

Bayan aukuwar lamarin, masu yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane sun mika Lin Hao zuwa asibitin yara na birnin Chengdu na lardin Sichuan ba tare da bata lokaci ba. A halin yanzu, Lin Hao ya riga ya sami sauki sosai, kuma ya cigaba da zama tare da iyayensa. Yayin da manema labaru suka tambaye shi menene burinsa a nan gaba, Lin Hao ya ce:

"Burina na lokacin da shi ne, ina so in ci jarrabawar shiga cikin jami'a, na fi son jami'ar Tsinghua wadda ke yin suna sosai a nan kasar Sin. Amma saboda akwai abokan karatu da malamai nawa da dama wadanda aka binne su cikin baraguzan gine-gine a sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa, shi ya sa burina na yanzu shi ne, in gina gidaje wadanda ke da karfi sosai wajen yaki da mummunan bala'in girgizar kasa."

Idan mu kwatanta shi da Lin Hao mai shekaru 9 da rabi da haihuwa, wani dalibin makarantar sakandare mai suna Xue Xiao, mai shekaru 17 da haihuwa, ya kara fuskantar wahalhalu. Yayin da mummunan bala'in girgizar kasa ke faruwa, Xue Xiao yana karatu a aji. Nan da nan ne ajinsa ya girgiza sosai har ya ruguje. An binne shi da abokan karatunsa a karkashin tarkacen gine-gine. A ranar 15 ga watan Mayu, da misalin karfe 7 da yamma, masu aikin ceto sun gano Xue Xiao da wata daliba daban dake kusa da shi. Ko da yake Xue Xiao ya ji mummunan rauni, amma ya bukaci masu aikin ceto da su ceci wannan yarinya tukuna. Daya daga cikin masu aikin ceto, sojan rundunar sojojin Beijing, kuma memban kungiyar masu yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane cikin gaggawa ta kasar Sin He Hongwei ya gaya mana cewar:

"A wancan lokaci, Xue Xiao yana cikin wani hali mai hadari sosai, saboda an dade an binne shi a karkashin baraguzan gine-gine. Yayin da mu masu aikion ceto muna yunkurin ceton wani mutumin da aka binne shi, idan yake barci, to, watakila ba zai farka ba har abada."

Domin bada kwarin-gwiwa ga Xue Xiao wajen tsayawa tsayin daka kan zamansa, He Hongwei ya rika yin magana da shi.

"Ya ce, me kake son ci? Na ce ina son cin ice-cream. Ya ce, to, kawu, zan saya maka? Na ce, to, da kyau, Na kuma cigaba da cewar, kada ka ji tsoro, kada ka yi barci. Bayan da na fito da kai, za ka sayo mini ice-cream. Ya ce, to, kawu, na gane. Daga bisani ne na tambaye shi, me kake son ci kuma? Ya amsa mini cewa, kawu, ba na son cin ice-cream. Na ce, to, menene kake so? Ya ce, coca-cola nike so."

A karshe dai, an mika Xue Xiao zuwa asibitin Huaxia na jami'ar Sichuan, inda aka yi masa tiyatar katse hannunsa na dama. Bayan da ya sami sauki kadan, a kan gadonsa a asibiti, Xue Xiao ya ga coca-cola da mutanen da suke jin tausayinsa suka saya masa, ya yi murmushi har ya ce, bayan da ya warke, zai cigaba da kokarin karatunsa, kuma yana son shiga cikin jami'a a nan gaba.

Bayan da kuka ji labarai dangane da dalibai Lin Hao da Xue Xiao, yanzu bari mu sanya muku wani labari game da wata malama mai shekaru 26 da haihuwa kawai. Malama Yuan Wenting, wata malama ce ta makarantar firamare ta dimokuradiyya ta garin Shigu na birnin Shifang. Yayin da mummunan bala'in girgizar kasa ke faruwa, malama Yuan Wenting ta fito da dalibanta daya bayan daya ba tare la'akari da hadarin da take fuskanta ba. Gaba daya dai Yuan Wenting ta ceto dalibai guda 13, wani dalibi mai suna Wu Jiahui da Yuan Wenting ta ceto ya yi kuka har ya ce: "Malama Yuan ta ajiye ni a kofar ajinmu, sa'annan ta sake shiga aji domin ceton sauran dalibai. Na ji muryar 'PENG!', sa'annan silin na ajinmu ya fado kasa! Na ga wani dalibin da malama Yuan ta runguma."

A ranar 12 ga watan Mayu, da misalin karfe 10 da dare, masu aikin ceto sun gano gawar malama Yuan Wenting, wadda aka binne shi a karkashin baraguzan gine-gine. Amma wannan malama mai jaruntaka sosai ta riga mu gidan gaskiya saboda mummunan rauni da ta ji, shekarunta ya kai 26 kawai! Masu yin amfani da hanyar sadarwa ta Internet na kasar Sin sun maida malama Yuan Wenting a matsayin wata malama mafi nagarta kuma mafi kyau-gani a nan kasar Sin.