Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-01 15:13:39    
An fara koyar da wasan Peking Opera a makarantun firamare da sakandare na birnin Tianjin

cri

Wakilinmu ya samu wannan amo ne daga wani darasin wasan kwaikwayo na waka na kasar Sin wato Pekin Opera da ake koyarwa a makarantar firamare ta titin Xiangjiang ta birnin Tianjin na kasar Sin. Tare da kide-kiden wasan Peking Opera da ake watsa a cikin na'urar daukar murya, Pan Xiaotong, wata 'yar makaranta tana yin wasan Peking Opera bisa jagorancin malami. Kuma ta gaya wa wakilinmu cewa, ta riga ta koyi wasan Peking Opera har shekaru fiye da biyu. Kuma ta kara da cewa,

"A ganina, yin wasan Peking Opera yana da ban sha'awa, kuma ina sha'awar kalmomin waka da ake rerawa a cikin wasan. Kafin mu koyi wasan Peking Opera, kullum malam Fan ya kan gaya mana wasu labarai game da wasan, ta haka za mu iya kara fahimtarsa da kuma koyonsa yadda ya kamata."

Kullum a kan kira birnin Tianjin "garin wasannin kwaikwayo na waka na kasar Sin", inda ake iya samun tushen fararen hula mai inganci na wasan Peking Opera. Yau da shekaru da dama da suka gabata, bi da bi makarantun firamare da sakandare da dama sun kaddamar da shigad da wasan Peking Opera cikin darussan koyar da wake-wake. A shekara ta 2005, makarantar firamare ta titin Xiangjiang ta birnin Tianjin ta tattara malamai wajen tsara littattafan koyar da wasan Peking Opera, da kuma kaddamar da ayyukan koyar da wasan. Yanzu ba kawai 'yan makarantar suna iya bayyana ilmi game da wasan ba, har ma suna iya rera wasu wakokin da ke cikin wasannin Peking Opera. Yang Qiuyue, wata malamar koyar da wake-wake ta bayyana cewa,

"Game da yaran da suka fara karatu ba da jimawa ba, wannan shi ne karo na farko da su san wasan Peking Opera, shi ya sa da farko muka yi amfani da wasu na'urorin zamani na koyarwa kamar bidiyo domin kara sha'awar da suka nuna wa wasan sannu a hankali."

Liu Lianqun, wani kwarare na wasannin kwaikwayo na waka na birnin Tianjin ya bayyana cewa, yanzu dimbin kasashe sun shigad da al'adun da ke da halayen musamman na kabilu cikin ilmi na matakin farko. Bisa wannan matsayi, shigad da wasan Peking Opera cikin darussa zai ba da taimako wajen gadon al'adun kabilu. Kuma ya kara da cewa,

"Mene ne nufin shigad da wasan Peking Opera cikin darussa? A ganina nufinsa shi ne horar da matasa daga makarantun firamare da sakandare domin su girmama da kuma lura da nagartattun al'adun kalibunsu, da kuma fahimtar fasahohin gargajiya na-gari namu, ta yadda za a iya yada al'adun kabilunmu daga zuriya zuwa zuriya, da kuma inganta karfin kasarmu na al'adu."

A idon Feng Jicai, sanannen marubuci kuma shugaban kawancen adabi da fasahohi na birnin Tianjin, shigad da wasan Peking Opera cikin darussan makarantun firamare da sakandare wani kyakkyawan mataki ne, amma a waje daya kuma ya ba da shawarar cewa, ban da wasan, ya kamata wurare daban daban na kasar Sin su kiyaye fasahohinsu na musamman domin shigad da dimbin fasahohin kabilu cikin darussa.(Kande Gao)