Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-30 15:08:42    
Ana raya sansanin noman kayayyakin lambu a kasar Sin cikin daidaici

cri

A cikin irin wannan hali ne, hukumar birnin Shouguang ta dauki wani mataki mai muhummanci don noman kayayyakin lambu cikin daidaici. Hukumar ta aika da kwararru zuwa kauyuka daban daban na birnin don jagorancin manoma da su noma kayayyakin lambu cikin daidaici. Sa'an nan ta kashe makudan kudade wajen kafa wata kyakkyawar cibiyar binciken ingancin kayayyakin lambu. Sakamakon binciken da cibiyar ke samu ya sami amincewa daga wajen kasashen duniya sama da 50. Malam Yin Yong, wani jami'in babban kamfanin raya aikin noma na zamani na birnin Shouguang ya ce, "kayayyakin lambun da muke samarwa suna samun karbuwa sosai daga wajen kasuwanni a yanzu. Don haka muna samun kudade masu yawa daga wajen kayayyakin lambun da muke sayarwa. Muna kara ba da kwarin gwiwa ga manoman da su yi noman kayayyakin lambu cikin daidaici."

Yanzu, Malam Wang Leyi, dagacin kauyen Sanyuanzhu na birnin Shouguang yana jagorancin manoma da su nuna himma wajen noman kayayyakin lambu cikin daidaici. Sa'an nan ya yi kira ga kamfanonin aikin noma na dukan kasar Sin da su ci gaba da noman amfanin gona cikin daidaici, don samar da kayayyakin noma masu inganci. Ya kara da cewa, "jama'a na dogara da abinci wajen zaman rayuwarsu, don haka samar da abinci mai inganci yana da muhimmanci sosai ga jama'a. Wajibi ne, a samar da kyakkyawan abinci mai inganci ga jama'a. Ya kamata, a yi kokari sosai wajen noman amfanin gona cikin daidaici. A sanya ido sosai a kan yadda ake noman amfanin gona, don ba da cikakken tabbaci ga samar da amfanin gona mai inganci da gina jiki ga dukan jama'a. "


1 2 3