Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-25 19:38:31    
Yawan kudin da kasar Sin ta samar domin tinkarar girgizar kasa ya kai fiye da RMB yuan biliyan 54.6

cri

Bisa labarin da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar, an ce, bisa ikon da babban ofishin ba da umurni kan fama da girgizar kasa da gudanar da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba shi, ya sanar da cewa, ya zuwa ran 25 ga wata da safe da karfe 12, yawan kudin da gwamnatoci na matsayi dabam daban na kasar Sin ta samar domin tinkarar girgizar kasa ya kai fiye da RMB yuan biliyan 54.6.

Bugu da kari kuma ya zuwa ran 25 ga wata da safe da karfe 12, yawan kudade da kayayyakin taimako da kasar Sin ta samu daga gida da waje ya kai fiye da Yuan biliyan 53.5, kuma yawan kudi da kayayykin da aka kebe ga wuraren da ke fama da bala'i ya kai fiye da RMB yuan biliyan 19.1.

Ya zuwa ran 25 ga wata da safe da karfe 12, girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ya riga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 69,185 yayin da mutane 374,171 suka jikata, kuma mutane 18458 suka bace.