Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-24 17:45:33    
Birnin Chongqing yana dora muhimmanci kan shigo da kwararru na-gari

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. Bisa matsayinsa na birnin da ke karkashin jagorancin gwamnatin kasar Sin kai tsaya daya tak a yammacin kasar Sin, a 'yan shekarun nan da suka gabata, birnin Chongqing ya dora muhimmanci sosai kan shigo da kwararru na-gari na gida da na waje. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu leka wannan birni tare.

Bisa matsayinsa na birni mafi sabuntaka da ke karkashin jagorancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye, birnin Chongqing yana ta samun saurin bunkasuwa wajen tattalin arziki a cikin jerin shekaru 7 da suka gabata. A cikin wannan birnin da fadinsa ya kai murabba'in kilomita 8.24, kuma yawan mutanensa ya kai miliyan 32, wani muhimmin dalilin da ya sanya bunkasuwar tattalin arzikinsa shi ne kwararru na-gari da suka zo daga wurare daban daban.

Chen Shu yana daya daga cikinsu. Shi ne shugaban kwalejin binciken kimiyyar zaman al'umma ta birnin Chongqing, kuma zaunannen mataimakin shugaban cibiyar nazari da kuma bunkasuwa ta gwamnatin birnin, haka kuma shi babban edita ne na mujallar "Gyare-Gyare" da ke dora muhimmanci kan bunkasuwar birnin Chongqing. Game da sauye-sauyen birnin, ya gaya mana cewa, "Ni ne na ganam ma idona wajen bunkasuwar birnin Chongqing. A cikin shekaru 10 da suka gabata, na iya gano sauyinsa a ko wane wata har ma a ko wace rana. Kullum idan wani ya dade yana wani wuri, lallai zai gaji da zama a nan, amma ya zuwa yanzu ina jin farin ciki sosai."

1 2