Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-21 20:06:25    
Gwamnatin kasar Sin ta bayar da kudin da yawansu ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 54.312, don yaki da bala'in girgizar kasa

cri
Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da rahoto cewa, ya zuwa ranar 21 ga wata da karfe 12, hukumomi na matakai daban daban na kasar Sin sun bayar da kudin da yawansu ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 54.312, don yaki da bala'in girgizar kasa da ceton jama'a. Kuma kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyakin da ke da darajarsu ta kai kudin Sin yuan biliyan 46.74 daga bangarori daban daban na gida da na waje, kuma an riga an bayar da taimakon kudi da na kayayyaki da darajarsu ta kai yuan biliyan 15.649 ga yankuna masu fama da bala'in.

Bisa rahoton da ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar an ce, ya zuwa ranar 21 ga wata da karfe 12, mutane 69,181 ne suka rasa rayukansu a sakamakon babbar girgizar kasa da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da 17,397 suka bace. (Bilkisu)