Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-21 16:32:12    
Masu aikin sa kai na gida da waje da suka shiga aikin yaki da bala'in girgizar kasa a Wenchuan sun kai miliyan 1.3

cri
Bisa labarin da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya samu daga kwamitin kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin a lardin Sichuan, an ce, bayan aukuwar bala'in girgizar kasa a gundumar Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin, yawan masu aikin sa kai na gida da waje wadanda suka shiga aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceton jama'a ya kai kimanin miliyan 1.3.

Wadannan masu aikin sa kai sun fito ne daga wuraren kasar Sin daban daban da kuma kasashen Canada da Amurka da Rasha da Japan da Singapore da sauransu.

An labarta cewa, a lokacin da ake yaki da bala'in don ceton jama'a bisa mataki na farko, masu aikin sa kai sun aiwatar da ayyukansu ne musamman domin neman wadanda ke da sauran numfashi don cetonsu daga buraguzen gine-gine, da yi wa marasa lafiya jiyya da rarraba wa jama'a kayayyaki a wuraren da bala'in girgizar kasa ya galabaita. Yanzu kuma suna shawo kan jama'ar da bala'in ya shafa don kwantar da hankulansu da yi musu rakiya yau da kullum. (Halilu)