Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-19 11:05:12    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin (I)

cri

Dan da ya fi nuna kauna ga mamarsa. Kwanakin baya gwamnatin Yangsuo na jihar kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta Guangxi ta kasar Sin ta daukaka wani mauzaninta mai suna Mo Rongchang wanda ya ke da shekaru 61 a matsayin dan wanda ya fi nuna kauna ga mamarsa. Mo Rongchang,nakasashe ne ya kula da mamarsa cikin shekaru masu yawa. Saboda kulawa da ya sa kan mamarsa,mamarsa ta yi bikin cika shekaru 105 da haihuwa. Mamarsa ta fadi kasa a shekara ta 2000 daga baya jikinta ya shanye. Duk da haka danta ya sa lura a kanta sosai. Wasu sun ce in babu danta,mamar ta mutu tun tuni. Ya dafa mata abinci ya ciyar da ita. Ya kuma wanke tutafinta da ba da taimako ga mamarsa da ta yi wanka kowace rana.

An yi kira da a ba da taimako ga yara marasa ubanni. Wakilan majalisu da suka zo daga lardin Guangdong da na yankin mulki na musamman na Hong sun bukaci gwamnatocin da su dauki matakan taimakon yara da aka haifa ba ta hanyar aure yadda ya kamata ba domin shawo kan wahalolin da suke sha. Bisa labarin da aka samu, an ce da akwai yaran da aka haifa ba ta hanyar aure yadda ya kamata ba sama da dubu hamsin a yankin delta na kogin Pearl na lardin Guangdong. Shekarunsu na tsakanin watanni biyu da shekaru sha hudu. Ubannin yaran mutanen Hongkong ne, uwayensu kuwa mata ne dake zama babban yankin kasa,saboda aka haife su ba ta hanyar yadda ya kamata ba shi ya sa suna fama da matsalar samun magani mai rahusa.

Karnuka sun sami 'yanci bayan wani hadarin mota. Wata babbar mota dake dauke da karnuka 626 ta kife a ranar lahadi a dab da Yanji da ke cikin lardin Jilin. Yawancin karnukan da aka sanya a cikin mota sun fice nan take. Da jin haushin karnukan, kauyawan dab da wurin hadari sun fito fili sun ba da taimako ga 'yan sanda. Wani jami'in 'yan sanda da ya yi kokarin tattara karnuka, har ma wani karen ya cije shi. Duk da haka,karnuka da dama sun fice,kashi 97 bisa dari aka tattara su daga bisani. Mai mota ya ce ya yi hassarar kudin Sin Yuan dubu dari sabo da wannan hadarin mota.

Wata jami'ar 'yan sanda ta sami kwarin gwiwa bayan da ta yi kallon sinima mai ban tsoro. Wan Rong,ita budurwa ce jami'ar sanda dake aiki yankin Xicheng na birnin Beijing, ita kuma mai razanawa ce bayan da ta kammala karatunta a jami'a, ta kara kwarin gwiwarta ta hanyar kallon sinima mai ban tsoro.A halin yanzu ta kara kwarewarta wajen binciken miyagun laifuffuka sabo da karfin zuciya da take da shi bayan ta yi kallon sinima mai ban tsoro. Ta ce ta razana kwarai da gaske yayin da ta yi wa wata gawar bincike a karo na farko daga baya ta yi mafarki mai ban tsoro.

Domin rage tsoron da take fama da shi, ta kuduri aniyar kallon sinima mai ban tsoro kamar The silence of the lambs. A kwana a tashi ta kware a aikinta na bincike gawwaki.

Mai tara abubuwa masu daraja ya sami tunaninsa. An sami wani mutum da ake kiransa Liu a birnin Taiyuan, babban birnin lardin Shanxi na kasar Sin, ya saye wani dutse mai daraja da nauyinsa ya kai TON hudu daga kasar Myanma duk domin kayatar da gidansa. Daga baya ya gane cewa da wuya a kiyaye wannan dutse cikin dakinsa, shi ya sa ya sake tunaninsa ya ajiye dutsen nan a haraba. Ya saye wannan dutse ne da kudin Sin Yuan dubu dari takwas a yan shekarun baya, ya kuma gayyaci mashahuran masaka da su saka zanen manyan duwatsu biyar da suka shaharaha a jikin dutsen. Domin kare dutsen daga masu sata,ya yi kiwon wasu karnuka da su yi yawo a haraha ban da wannan kuma ya sanya wani tsarin tsaro a gidansa. Mutane da yawa suna sha'awar wannan dutse mai daraja da ya tanada a harabarsa.

Wani yaro ya yi karya domin samun aikin yi. An sami wani yaro mai suna Liu dake da shekaru 15 da haihuwa a kauyen Chibi wanda ba ya so karatu a makarantar middle school yana so ya samu wani aikin yi. Yaron ya bukaci wani abokinsa mai suna Xu da ya buga waya zuwa ga iyayensa a ranar jumma'a cewa an yi garkuwa da shi. Da jin haka, uban Liu ya kirawo 'yan sanda, 'yan sanda sun yi bincike dalla dalla a kauye kuma sun yi hira da mai gabatar da rahoto Xu. Ba da dadewa ba an bankado shirin da yaron Liu ya shirya. Ya ce " ba na so in yi karatu a makaranta ina so in samu aikin yi. na sani iayena ba su yarda da haka,sai na yi karya."

Harshen rashanci ya taka rawar gani a jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta. Mr Joshua Kucera, dan kasuwa ne da ya zo daga kasar Rasha yana jin dadi yayin da yake bakunci a birnin Urumqi,babban birnin jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta dalili kuwa shi ne mutane da yawa sun gane abin da ya ke nufi yayin da yake magana da harshen rashanci. Harshen Rashanci ya samu maraba sosai saboda kasuwancin da ake yi a wannan birnin tsakanin kasar Sin da kasashen Rasha, da Uzbekistan, da Kyrgyzstan da Kazakhstan a cikin shekarun baya. Bisa labarin da wani kwararre kan cinikin kasa da kasa ya samar, an ce mutanen dake nazarin harshen rashanci ya fi na wadanda ke nazarin turanci yawa a wannan birni, duk wanda ya kware kan rashanci da sauki ya samu aikin yi.

Wata mata da ta fi tsufa a jihar Tibet ta kasar Sin. An sami wata mata mai suna Amai Ciren da ta fi tsufa a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin wadda shekarunta ya wuce 117 da haihuwa. Ma'aikatan hukuma na gundumar Linzhou ta jihar Tibet sun tattara mutanen dake cikin kauyenta da suka yi bikin murnar ranar cikon shekaru 117 da haihuwa. Wasu 'yan kasuwa ma sun bayar da kyautar kudi dominta. An haifi Amai Ciren a ran 16 ga watan Maris na shekara ta 1891, tana da 'ya'ya guda hudu. Daga cikinsu wadda diyarta ta biyu ta fi tsufa ta kai shekaru 69 da haihuwa,ita ma tana zaman rayuwa yadda ya kamata. Da aka tabo batun tsawon rayuwa, matar ta ce 'yanayin zaman rayuwa na kara kyautatuwa da kuma sharudan kiwon lafiya na kara inganta. Bisa kididdigar da hukumar da abin ya shafa ta bayar, an ce kwatankwacin tsawon rai na kowane mutum na jihar Tibet ya karu har ya kai shekaru 67 da haihuwa daga shekaru 35.5 a shekara ta 1959 yayin da aka yantar da Tibet cikin lumana. Mutanen da shekarunsu ya wuce da dari sun karu a jihar Tibet a halin yanzu.

Wata yarinya ta yi shirin yin dogon gudu daga Tibet zuwa birnin Shanghai. Wata yarinya da ake kiranta Zhang Huimin mai shekaru 9 da haihuwa a lardin Hainan na kasar Sin ta yi shirin yin dogon gudu daga Tibet zuwa birnin Shanghai,birni mafi girma da ya fi samun ci gaban masana'antu a kasar Sin. Mahaifin Yarinya ya ce " mun yi shiri sosai, za mu fara gudu a farkon watan Afril. Za mu fara daga wata gada ta sada zumuncin da ta hada kasar Nepal da Tibet ta kasar Sin. Za mu yi gudu na tsawon kilomita hamsin a kowace rana, idan diyata ba ta ji dadi a kan hanya za mu dakata a duk lokacin da muka ga dama." Wannan yarinya ta taba yin gudun zagaya lardin Hainan a watan Janairu na shekara ta 2007, ta yi dogon gudu na tsawon kilomita dubu hudu daga lardin Hainan zuwa birnin Beijing a watan Augusta na shekara ta 2007. wannan gudu dga Tibet zuwa Shanghai karo na uku ne da ta yi dogon gudu a kasar Sin.

Masoya sun yi yunkurin kashe kansu. Masoya biyu da suka nuna wa juna soyayya maras iyaka sun sami matsala,sai sun kudurin aniyar kashe kansu. Duk da haka matar ta rayu. A ranar jumma'ar da ta shige, wani mai masaukin baki dake cikin wani kauye ya ga baki biyu da suka tsintsi kansu cikin mawuyancin hali, sai ya buga waya zuwa ga ofishin 'yan sanda na gundumar Xishan ta lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin. Da 'yan sanda sun isa wurin, tare da taimakon likitoci, sun gano cewa masoya biyu sun sha kwayoyi masu guba. Likitocin sun warkar da matar da ta suma,amma masoyinta ya mutu saboda ya sha kwayoyi masu guba da yawa. Dalilin da ya sa masoyan sun kashe kansu ne domin iyayensu ba su amince da aurensu ba.

Manoma a yankin Baoji sun gano tsuntsaye masu jan baki a wurinsu. Kwanakin baya wasu manoma sun gano tsuntsaye biyu masu jan baki a yankin Baoji na lardin Shaanxi,ko da ya ke akwai irin tsuntsaye a wannan yanki amma babu daya daga cikinsu yake da jan baki, shi ya sa mutanen wurin sun yi mamaki. Wani manomi mai suna Zhao Qi ya gano tsuntsayen ne yayin da yake noma,tsuntsayen suna tafiya a sararin sama bisansa da ganin haka ya sanar da ofishin kula da kungurmin daji. Ma'aikatan ofishin sun ce a kan samu irin tsuntsaye a gabaci da kudanci da kuma tsakiyar kasar Sin ba a yankin arewa maso yammacin kasa ba. Mutanen da abin ya shafa sun fara sa ido kan irin tsuntsaye masu jan baki.

Wani da ya ba ubansa mamaki. Wani mutum nmai suna Lu Yibo ya sami dan suna sabo da ya bukaci jaridu biyu na wurin da su buga talla na shafuna biyu duk domin murnar ranar haihuwa ta ubansa a birnin Zhengzhou,babban birni na lardin Henan. Mr Lu,dan kasuwa ne, ya yi shirin yin talla a cikin jaridu kafin watanni biyu. Ubansa mai shekaru hamsin da haihuwa bai san shirinsa ba da ya bude jarida ya ga talla da aka buga a cikin jarida domin murnar ranar haihuwarsa ya yi mamaki kuma ya yi farin ciki. Mr Lu ya ce yana so ya ba ubansa mamaki ta wata hanyar musamman duk domin nuna kauna da girmamawa ga ubansa. Duk da haka ba dukkan mutanen da suka ganin jarida sun yi masa yabo ba,wasu sun ce ya yi hakan nan ne domin samun suna kawai.

An samu abin mamaki wajen wani tsoho. An sami wani tsoho mai suna Wu Dechen wanda ya ke da shekaru 97 da haihuwa a birnin Hengyang na lardin Hunan na kasar Sin.kwanakin bay sabbin hakori biyu sun fito a bakinsa da kuam farin gashinsa ya zama na baki.an ce abin mamaki ga tsofo.Mr Wu,ma'aikaci ne da ya yi ritaya tun tuni a garin Dapu na mallakar birnin,jikinsa ya shanye, shi ya sa ya kan zauna kan kujera mai kafafuwa. Kuma ba shi da hakora ko daya a wannan lokaci. Likita mai kwarewa na asibitin jama'a na lardin Hunan Mr Zhang Chi ya ce sabbin hakorin da Mr Wu ya samu kwanan baya yana bayyana cewa yana da koshin lafiya amma ba ya nufi ya koma matashi ba.Diyar Wu ta ce ubanta ya kai yi hawan dutse har zuwa shekarar da shekarunsa ya kai 80. bayan da jikinsa ya shanye ba ya ci nama ya fi son cin abincin cincin da cake da 'ya'yan itatuwa da kuma madara.

Wani mutum da ya ta da fitina a wurin taruwar jama'a. A ranar jumma'a da ta shige, 'yan sanda na birnin Fuzhou,babban birni na lardin Fujian sun kama wani mutum da da ke amfani da bulo da wuka tare da yin kuwwa don gwada karfinsa,har ma ya zama barazana ga matafiya. Da ganin haka 'yan sanda sun tsare shi. Yayin da 'yan sanda ke kokarin tsare shi,ya yi amfani da bulo domin kai bugu kan motar dake dauke da 'yan sanda,sai 'yan sanda sun tuka motar waje,mutumin ya yi yunkurin kama mota. Daga baya 'yan sanda sun kama shi kuma sun kai shi cajin ofishi.

Bisa labarin da aka samu, an ce mutumin nan ya sha kwaya shi ya sa ya aikata haka.

Wani dalibi ya yi babbar hassara a kasuwar hada hadr kudade. Kwanan baya wani dalibin da ya yi babbar hassara a kasuwar hada hada kudade ya gaza zama yadda ya kamata, sai ya ci abinci maras gina lafiyar jiki. Kamar yadda sauran da daliban da suka shiga kasuwar hada hadar kudade

Suke, dalibin nan mai suna Qian Wu ya fada cikin wani mawuyancin hali saboda kasuwar hada hadar kudi ta yi tashin da sauka ba fashi a cikin kwanakin baya,shi ya sa da yada daga cikinsu sun yi hassara.