Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-19 10:39:15    
'Yan kabilar Tatar da ke mayar da hankali kan aikin ba da ilmi, musamman ma aikin ba da ilmi na gida

cri

Kabilar Tatar ita ce wata kabila ce da yawan mutanenta ya fi karanci a cikin kabilu masu bin addinin musulunci da suke zama daga zuriya zuwa zuriya a shiyya mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur ta jihar Xinjiang, ita ce kuma wata kabila mai mutane kadan a cikin duk kananan kabilu 55 a kasar Sin, yawan mutanen kabilar ya kai kamar 6000, suna zama a wurarre daban daban na jihar Xinjiang. Ko da ya ke mutanen kabilar Tatar ba su da yawa, amma al'adun harshen kabilar yana kiyaye abin musamman nata, kuma babu jahilci tsakanin balagagu, dalilin da ya sa haka shi ne, kullum 'yan kabilar Tatar suna mai da hankali kan aikin ba da ilmi, musamman ma aikin ba da ilmi na gida. Kwanan baya, wakilinmu ya je birnin Yiing na jihar Yili mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hazak ta Xinjiang, domin kai ziyara ga Iliyar, wani tsoho 'dan kabilar Tatar, wanda ke yin aikin ba da ilmi a duk rayuwarsa.

Iyalin Iliyar yana wani karamin yadin da ke arewacin birnin Yining, a lokacin da ake ambatar aikin ba da ilmi na gida na kabilar Tatar, malam Iliyar, wanda yawan shekarunsa na haihuwa ya kai 72 ya ce, "Ko da ya ke yanzu ba a kafa makarantun koyon harshen kabilar Tatar na musamman ba, amma kullum muna kiyayen al'adun harshen Tatar. Mu fara wannan aiki ne daga aikin ba da ilmi na gida. Kamar misali: yaran da yawan shekarunsu na haihuwa ya kai kamar uku ko hudu, suna iya fahimta da magana da harshen Tatar, ko da ya ke ba su shiga makaranta ba."

Malam Iliyar yana ganin cewa, al'adun harshe ita ce muhimmiyar alama ta wata kabila, ya kamata ko wace kabila ta gaji yada al'adun harshenta. Dalilin da ya sa dukan 'yan kabilar Tatar suke iya magana da harshen Tatar shi ne, kabilar tana mai da hankali kan aikin ba da ilmi na gida, gida kuma ya gabatar da wani muhalli mai kyau wajen koyon harshen.


1 2 3