Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-16 18:29:04    
Kasar Sin ta bayar da kudin da yawansu ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 53.864, don yaki da bala'in girgizar kasa

cri

Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da rahoto cewa, ya zuwa ranar 16 ga wata da karfe 12, hukumomi na matakai daban daban na kasar Sin sun bayar da kudin da yawansu ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 53.864, don yaki da bala'in girgizar kasa. Kuma kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyakin da ke da darajar kudin Sin RMB fiye da yuan biliyan 45.7 daga bangarori daban daban na gida da na waje, kuma an riga an bayar da taimakon kudi da na kayayyaki da ke da darajar kudin Sin RMB sama da yuan biliyan 14.2 ga yankuna masu fama da bala'in.

Bayan haka kuma, ya zuwa ranar 16 ga wata da karfe 12, mutane 69170 ne suka rasa rayukansu a sakamakon babbar girgizar kasa da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da 17426 suka bace. (Bilkisu)