Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-11 20:33:11    
An yi kusan kawo karshen aikin ba da agaji bisa babban mataki wajen likitanci ga wurare masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan

cri

Kakakin ya bayyana cewa, ba da tabbaci ga rashin samun yaduwar annoba aiki ne mai muhimmanci a cikin ayyukan kiwon lafiya na wannan matakin lokacin bayan girgizar kasa, yanzu ana nan ana yin ayyukan yin rigakafin yaduwar annoba da sa ido kan aikin kiwon lafiya a wurare masu fama da bala'in girgizar kasa. Ya zuwa ranar 10 ga wannan wata, a wurare masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan, ba a sami lamarin kiwon lafiyar jama'a da yaduwar annoba ba.

Kodayake hakan ake yi, amma, wannan jami'in ya bayyana ba tare da boye kome ba cewa, a halin yanzu a wurare masu fama da bala'in girgizar kasa, da akwai hadarin yaduwar annoba da zai auku cikin tsanani , game da wannan, sassan kiwon lafiya sun riga sun yi shiri sosai. Ya bayyana cewa, da farko, matsugunan da aka kafa domin wadanda suke fama da bala'in girgizar kasa. Dayake an kafa jama'a masu fama da bala'in girgizar kasa matsugunai a cunkushe, shi ya sa aka kara damar samun aukuwar hadarin yaduwar annoba. Yanzu, mun riga mun kara karfafa ayyukan sa ido a kan ayyukan kiwon lafiya na wadannan matsugunai. Na biyu, bisa fasahohin da aka samu a da, bayan aukuwar babban lamarin girgizar kasa, tamkar yadda aka yi a wannan gami, ingancin ruwan sha da abinci na da muhimmanci sosai, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta yi hadin guiwa da sassan da abin ya shafa don sa ido kan ingancin ruwan sha daga mafarin samunsa zuwa lokacin da ake sha.

Yanzu, ma'aikatar kiwon lafiya ta riga ta sami rahotannin da aka samar mata dangane da cutar fuka da cutar hanta da cutar gudawa da sauransu, amma ba a sami  aukuwar lamarin kiwon lafiyar jama'a da yaduwar babbar annoba a wurare masu fama da bala'in girgizar kasa ba.(Halima)


1 2