Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-11 17:12:15    
Mutane 69146 sun rasa rayukansu a cikin girgizar kasa ta Wenchuan a Sichuan ta kasar Sin

cri

Ran 11 ga wata, bisa urmunin da babban ofishin ba da jagoranci ga ayyukan fama da bala'in girgizar kasa da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gabatar da cewa, ya zuwa ran 11 ga wata da tsakar rana da misalin karfe 12, mutane 69146 ne suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa ta Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da wasu fiye da dubu 370 suka jikkata, sa'an nan kuma, wasu 17516 sun bace.

Bisa rahoton da ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa ran 11 ga wata da tsakar rana da misalin karfe 12, kasar Sin ta karbi kayayyakin taimako da kuma kudaden tallafi fiye da kudin Sin yuan biliyan 44.5 daga rukunoni daban daban na zaman al'ummar kasa na gida da na waje, kuma ta riga ta karbar yuan biliyan 42.4 a hannunta.

Kazalika kuma, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta ba da rahoto da cewa, ya zuwa ran 11 ga wata da tsakar rana da misalin karfe 12, hukumomi na matakai daban daban sun zuba kudin Sin yuan fiye da biliyan 23.6 domin fama da bala'in girgizar kasa da kuma ayyukan ceto.