Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-09 21:21:01    
Mutane 69,142 ne suka mutu sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan

cri

Bisa labarin da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar, an ce, bisa ikon da babban ofishin ba da umurni kan fama da girgizar kasa da gudanar da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba shi, ya sanar da cewa, ya zuwa ran 9 ga wata da safe da karfe 12, girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ya riga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 69,142 yayin da mutane fiye da dubu 370 suka jikata, kuma mutane 17551suka bace.

Ya zuwa ran 9 ga wata da safe da karfe 12, yawan kudade da kayayyakin taimako da kasar Sin ta samu daga gida da waje ya kai fiye da Yuan biliyan 44.1, kuma an riga an samar da Yuan biliyan 13.7 gada adadin zuwa wuraren da ke fama da bala'in.

Bugu da kari kuma ya zuwa ran 9 ga wata da safe da karfe 12, kasar Sin ta kebe kudaden Sin fiye da Yuan biliyan 23.4 wajen fama da girgizar kasa. A cikinsu, yawan kudin da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta samar ya kai fiye da Yuan biliyan 18.9.