Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-09 20:45:26    
Mata masu son sakar siliki na kabilar Li ta kasar Sin

cri

Kabilar Li tana da mutane mafi yawa daga cikin kananan kabilun lardin hainan na kasar Sin, daidai kamar yadda sauran kananan kabilu suke, kabilar Li tana da al'adu masu halayen musamman nata, silikin kabilar Li mai kayatarwa shi ne kayan fasaha mai daraja da mata 'yan kabilar Li suka saka da hannayensu.

A dukkan lokutan da ake karbar manyan baki, mata 'yan kabilar Li sukan saye da dogayen skirt masu kyaun gani, suna rera wakoki masu dadi domin maraba da zuwan bakin, kuma su ne suka dinka wadannan dogayen skirt masu launuka daban-daban da irin silikin kabilar Li da suka saka."

Madam Wang Xuebing wadda take da shekaru 32 da haihuwa gidanta tana kauyen Shina na garin Chongshan da ke birnin Wuzhishan na lardin Hainan, tun lokacin da take da shekaru fiye da 10 da haihuwa ta fara koyon fasahar sakar siliki na kabilar Li, yanzu ta riga ta zama wata kwararriya ce wajen sakar siliki a cikin kauyen. Ta bayyana cewa, "Lokacin da nake da shekaru 10 da haihuwa, na ga sauran mutane da suke sakar siliki, daga baya na roke su don su taimake ni wajen sanya zare a hancin allura, ni ma na fara yin sakar, suna kallo a gefena kuma suna yi mini jagoranci. Sabo da na yi sha'awa sosai kan sakar siliki, shi ya sa na shafe mako daya kawai ina koyon aikin, kuma na fahimci abin da aka koya mini."

Yawan mutanen da suka shafe mako daya kawai suna koyo kuma sun fadakar da kansu kan fasahar sakar silikin kabilar Li kamar yadda madam Wang ta yi kadan ne, yawancinsu suna bukatar kara yin koyo har lokacin da ya kai kusan wata daya, za su iya rike fasahar sakar silikin kabilar Li da gaske.

Zaman rayuwar madam Wang ya ba da misali ga yawancin mata 'yan kabilar Li. A lokacin da ake shan aikin gona, sukan yi aikin noma da kiwon aladai da yanke roba, a lokacin hutun aikin gona kuma, sukan yi sake-saken silikin kabilar Li, kuma sun kulla kwangila da kamfanin da abin ya shafa don sayar da silikan da suka saka, ta haka ne suka samu kudin shiga don ba da taimako ga zaman yau da kullum na iyalansu. Madam Wang Yuebing ita ma ta taba shafe wani lokaci tana aiki cikin ofishin binciken fasahar sakar silikan kabilu na lardin Hainan. Ta ce, "Wancan kamfani wani kamfanin binciken fasahar musamman ne wajen sakar silikan kabilu, akan nuna kayayyakin silikin da aka saka ko kuma sayar da su ga kasashen waje, ciki har da Amurka da Japan. A da 'yan kasuwa sukan je gidajenmu don sayen dogayen skirt da muka saka, amma yanzu mun kulla kwangila da ofishin sakar siliki, 'yan kasuwa sukan yi odar kayayyakin siliki da muka saka daga wajen kamfanin."

Madam Wang ta bayyana cewa, kamar yadda take yi, matan da suke sakar dogayen skirt a lokutan da ba na aiki ba, sun iya sakar dogayen skirt 2 ko 3 a kowane wata, farashin kowanensu kuma ya kai kudin Sin Yuan darurruwa.

An ce, sabo da yawan mutanen da suke iya sarrafa irin wadannan tsoffin injunan saka yana ta raguwa, shi ya sa yawan silikin kabilar Li shi ma yana ta raguwa. Yau da shekaru 2 da suka wuce, karo na farko ne kasar Sin ta shigar da fasahar gargajiya wajen saka da kuma rinin sikilin kabilar Li cikin abubuwan al'adun tarihi da aka gada daga kakanni zuwa kakanni bisa matsayin kasar, sabo da haka ana ta kara mai da muhimmanci kan ayyukan cin gado da kuma yayata wannan fasahar gargajiya. Madam Huang Jinlian, direktar hadaddiyar kungiyar mata ta kauyen Shina na garin Chongshan da ke birnin Wuzhishan na lardin Hainan ta bayyana cewa, "Ina fatan za a kara ba da shawara domin kiyaye al'adun kabilar Li, kuma ina fatan mutanen wadanda sai kara karuwa suke za su koya kuma su rike fasahar sakar silikin kabilar Li, kada a batar da wannan al'adun gargajiya na kabilar Li".