Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-08 20:16:39    
Mutane 69136 sun mutu sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan

cri
Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba da labari bisa umurnin babban ofishin ba da umurni kan fama da girgizar kasa da gudanar da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar, cewa ya zuwa karfe 12 na ran 8 ga wata da rana, bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 69136 yayin da mutane fiye da dubu 370 suka jikkata, kuma mutane 17686 suka bace.

Kuma ya zuwa karfe 12 na ran 8 ga wata da rana, yawan kudade da kayayyakin taimako da kasar Sin ta samu daga sassa daban daban na gida da na waje ya kai kudin Sin wato Yuan biliyan 44, kuma an riga an kebe kudade da kayayyaki da yawansu ya kai Yuan biliyan 13.6 zuwa yankunan da ke fama da bala'in.

Ban da wannan kuma ya zuwa karfe 12 na ran 8 ga wata da rana, gwamnatoci na matakai daban daban na kasar Sin sun riga sun kebe kudade Yuan biliyan 23.4 wajen fama da bala'in.(Kande Gao)