Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 21:26:00    
Mr. Wen Jiabao ya bukaci a dauki matakai tun da wuri domin kawar da hadarin tafkin da ya samo asali daga girgizar kasa da ta yi a yankin Tangjiashan

cri

A ran 6 ga wata, firaministan kasar Sin, kuma babban kwamandan babbar hedkwatar bada umurni ga aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya ci gaba da yin rangadin gani da ido kan aikin kawar da hadadin tafkin da ya samo asali daga girgizar kasa da ta yi a yankin Tangjiashan. Mr. Wen ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su dauki matakai tun da wuri, bisa ka'idojin zaman lafiya da kimiyya, domin kawar da kalubale daga tafki mai shinge da ke Tangjiashan.

Mr. Wen ya fadi cewa, a halin yanzu dai, dukkan kasashen duniya suna mai da hankali kan ayyukan fama da tafki mai shinge da ke Tangjiashan, kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa su dauki hakikanan matakai bisa tushen zaman lafiya. Ya kamata a yi nazari sosai, da kuma tsara wasu shirye shirye domin tinkarar kalubale da mai yiyuwa ne zai faru. Abubuwan da suka fi muhimmanci su ne zaman lafiya na jama'a, da kuma yadda za a hana gurbacewar ruwa. Ya kamata a lura da sababbin matsaloli da za a gamu da su, domin kara kayutata shirin da aka tsara a da, ta yadda za a iya samu sakamako mai kyau.(Danladi)