Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 19:14:55    
An samu marayun da yawansu ya kai sama da 1000 a sanadiyar babbar girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan

cri
Yau 6 ga wata a nan birnin Beijing, wani jami'in da abin ya shafa na ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ya ce, bisa kididdigar da ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta lardin Sichuan ta yi da ba ta cikakke ba, ya zuwa ranar 5 ga wata, an samu marayun da yawansu ya kai sama da 1000, a sanadiyar babbar girgizar kasa da ta auku a lardin, ciki har da wasu yaran da har zuwa yanzu ba a tabbatar da asalinsu ba.

A gun wani taron manema labaru da aka shirya a ranar 6 ga wata, Mr. Zhang Shifeng, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin jin dadin jama'a na ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu hukumomin kula da harkokin jama'a suna aikin tabbatar da asalin marayun da ke yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa cikin gaggawa, kuma suna kara saurin tsugunar da marayu da bayar musu taimako. Ya zuwa yanzu, hukumomin kula da harkokin jama'a bisa matsayi daban daban ba su soma gudanar da aikin rikon marayu ba. (Bilkisu)