Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 19:14:54    
Sin ta soma tsara shirin sake gina yankunan da bala'in girgizar kasa ta shafa

cri

Wani jami'i daban mai suna Tang Kai na ma'aikatar kula da harkokin giaje da raya birane da kauyuka na kasar Sin shi ma ya fayyace cewa : ' Bisa bukatar da gwamnatin tsakiya ke da akwai ne, za a dauki shekaru takwas wajen sake gina yankunan da bala'in girgizar kasar ya shafa'.

Sa'annan ya fadi cewa, a duk yunkurin farfado da yankunan da bala'in ya shafa, sassan da abin ya shafa za su kyautata shirin sake gina yankunan duk bisa hakikanin halin da ake ciki. Shugabannin kasar Sin sun lashi takobin cimma wannan babban buri cikin lokaci yayin da suke tattara karfin da dukkan jama'ar kasar da suke da shi. ( Sani Wang)


1 2 3