Wani jami'i daban mai suna Tang Kai na ma'aikatar kula da harkokin giaje da raya birane da kauyuka na kasar Sin shi ma ya fayyace cewa : ' Bisa bukatar da gwamnatin tsakiya ke da akwai ne, za a dauki shekaru takwas wajen sake gina yankunan da bala'in girgizar kasar ya shafa'.
Sa'annan ya fadi cewa, a duk yunkurin farfado da yankunan da bala'in ya shafa, sassan da abin ya shafa za su kyautata shirin sake gina yankunan duk bisa hakikanin halin da ake ciki. Shugabannin kasar Sin sun lashi takobin cimma wannan babban buri cikin lokaci yayin da suke tattara karfin da dukkan jama'ar kasar da suke da shi. ( Sani Wang) 1 2 3
|