Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 10:47:22    
Bala'in girgizar kasa ya jawo wa masana'antun kasar Sin hasarar kudin Sin Yuan sama da biliyan 200

cri
Bisa kidayar da ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta yi, an ce, bala'in girgizar kasar da ta auku a lardin Sichuan na kasar Sin ya jawo wa masana'antun kasar hasarar kudin Sin Yuan sama da biliyan 200.

Daga cikinsu, yawan kudin da masana'antun lardin Sichuan sama da dubu 20 suka yi hasararsa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 201.1, haka kuma yawan kudin da masana'antu da mahakan ma'adinai na lardin Shaaxi suka yi hasararsa ya wuce kudin Sin Yuan biliyan 1.6, ban da wadannan kuma yawan kudin da masana'antu da mahakan ma'adinai na lardin Gansu suka yi hasararsa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 20.

Jiya Alhamis, wani jami'in ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar ya bayyana a birnin Beijing cewa, daga farkon binciken da aka yi, an gano cewa, masana'antun da aka riga aka farfado da su a yanzu ko a cikin wata guda mai zuwa ya dauki misalin kashi 51 cikin dari bisa dukan masana'antun da suka lalata a cikin bala'in, haka kuma sauran masana'antun da za a farfado da su zai kai kashi 25 cikin dari. (Halilu)