Hukumar binciken kudi ta kasar Sin ta ce, a ran 20 ga watan Yuni, za ta sanar da sakamakon binciken da ta yi na karo na farko kan kudin taimakon da aka kashe domin tinkarar bala'in girgizar kasa.
Ya zuwa ran 5 ga wata da karfe 12 na safe, yawan kudin taimako da kayayyakin da kasar Sin ta karbi ya daga fannoni dabam daban na gida da na waje ya kai fiye da RMB yuan biliyan 43.7. tun daga farkon aukuwar bala'in girgizar kasa, hukumar binciken kudi ta fara gudanar da ayyukansu domin tabbatar da a kashe kudin taimako da yin amfani da kayayyaki "yadda ya kamata" a "ko wane lokaci".
Mr. Wang Zhongxin direkatan ofishin binciken kudin ba da tabbaci ga zaman a'umma na hukumar binciken kudi ya ce, yanzu, yawan ma'aikatan da ke binciken kudin taimako da aka kashe domin tinkarar bala'in ya kai fiye da dubu 6.
Mr. Wang Zhongxin ya ce, nan gaba, hukumar binciken kudi za ta sanar da sakamakon bincike a ko wane wata, ta haka za a iya sanin yadda aka kashe kudin taimako.
|