Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 20:39:48    
Taron kwamitin dindindin na ofishin siyasa na JKS kan ayyukan sake gina yankin Wenchuan bayan bala'in girgizar kasa ta hanyar bada gudummawa tsakanin sassa iri daya na hukumomi daban-daban

cri

An labarta cewa, kwamitin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ya kira zamansa yau Alhamis a nan Beijing domin nazarin ayyuka sake gina yankin Wenchuan na lardin Sichuan bayan bala'in girgizar kasa ta hanyar bada gudummawa tsakanin sassa iri daya na hukumomi daban-daban. Babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Mr. Hu Jintao ya shugabanci taron, wanda ya nuna cewa, babbar girgiza kasa da ta auku a wannan gami, wata girgizar kasa ce mafi muni da ta fi janyo barna tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin. Aikin sake gina yankunan da abin ya shafa bayan bala'in, wani babban aiki ne mai wuya. Saboda haka ne, ake bukatar tattara karfin daukacin 'yan kasar; kuma ya kamata a bi hanyar bada gudummawa tsakanin sassa daban-daban masu kama.

Sa'annan taron ya nemi larduna da biranen da abin ya shafa dake daukar nauyin bada gudummawa ga yankunan da bala'in ya shafa da su samar musu leburori ,da kayayyaki da kudi har da bada shawarwari yayin da suke nuna fifiko a fannin kyautata yanayin rayuwar jama'ar wadannan yankunan da bala'in ya rutsa da su, da kuma taimaka musu wajen sake farfado manyan ayyukan tushe da gina na'urorin amfanin jama'a, da gidajen kwana da bada hidimomi a fannin horar da kwararru da kuma kimiyya da fasaha. ( Sani Wang )