Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 19:10:51    
Mutane 69127 ne suka rasa rayukansu a sakamakon babbar girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan

cri
A gun taron manema labaru da aka shirya a yau 5 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Guo Weimin, kakakin ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya sanar da cewa, bisa rahoton da ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar ta bayar, ya zuwa ranar 5 ga wata da karfe 12, mutane 69127 ne suka rasa rayukansu a sakamakon babban girgizar kasa da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da mutane 17918 suka bace. A jimilce, yawan mutanen da wannan bala'in mafi muni ya rutsa da su ya zarce miliyan 45 da dubu 710.

Mr. Guo Weimin ya ce, ya zuwa ranar 5 ga wata da karfe 12, kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyakin da ke da darajar kudin Sin RMB sama da biliyan 43.7 daga bangarori daban daban na gida da na waje, kuma an riga an bayar da taimakon kudi da na kayayyaki da ke da darajar kudin Sin RMB sama da biliyan 23.1 ga yankuna masu fama da bala'in. (Bilkisu)