Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 16:43:06    
Yara 84 na kabilar Qiang da ke gundumar Wenchuan inda girgizar kasa ta shafa sun je birnin Shenzhen domin ci gaba da karatu

cri
A ran 4 ga wata, yara 84 na kabilar Qiang wadanda suka zo daga gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan inda girgizar kasa ta shafa sun je sansanin tsaron iyakar kasa dake birnin Shenzhen na kasar Sin, kuma za su shafe watanni 3 ko fiye suna yin karatu a nan har zuwa ranar da za a kammala aikin gina makaranta a garinsu.

An ce, wadannan yara 'yan kabilar Qiang su 'yan makaranta ne masu talauci wadanda suka zo daga aji na farko har zuwa na 6 na wata makarantar firamare da ke gundumar Wenchuan, a lokacin da suke karatu a sansanin soja na runduna ta 7 na tsaron bakin iyakar kasa dake lardin Guangdong, rundunar soja da kungiyar nuna jin kai ta birnin Shenzhen za su yi kokarin samun malaman koyarwa na makarantun firamare da na sakandare na birnin da kwararrun hukamar tallafin mutane masu fama da bala'in ilmin halin dan Adam musamman domin ba da taimako ga wadannan yara. (Umaru)