Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 16:14:43    
Yiyuwar fashewar madatsar ruwa ta tafkin da girgizar kasa ta shafa tana karuwa

cri
Bisa labarin da muka samu daga ofishin ba da umurni kan kawar da hadarin tafkin da girgizar kasa ta shafa a Tangjiashan, an ce, ya zuwa yanzu yawan ruwan da ke cikin tafkin da girgizar kasa ta shafa ya riga ya zarce cubic-mita miliyan 200, tsayin doron ruwan ya zarce mita 70, kuma ruwan yana kwararewa daga cikin bangon madatsar ruwa. Sabo da kananan girgizar kasa da yawan ruwan sama da aka samu daga bangaren sama na kogin da kuma yanayin kasa na madatsar ruwa da dai sauran dalilan da ba a iya tabbatar da su ba, yiyuwar fashewar madatsar ruwa ta tafkin da girgizar kasa ta shafa tana karuwa.

Tangjiashan yana kusa da gundumar Beichuan, bayan aukuwar girgizar kasa a ran 12 ga watan Mayu, an toshe kogin Jianjiang sakamakon zaizayewar kasa daga tsaunuka, ta haka wani tafki mai matukar girma ya bullo.

Kuma an labarta cewa, daga ran 31 ga watan Mayu, an riga an kaurar da fararen hula fiye da dubu 250 daga birnin Mianyang da ke bangaren kasa na Tang jiashan.(Kande Gao)