Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 10:47:31    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Yawan mutanen lardin Henan na kasar Sin zai wuce miliyan dari.Lardin Henan wanda ya fi ko wane lardi yawan mutane a kasar Sin ya samu karuwar mutane.Ana sa ran cewa yawan mutanensa zai wuce miliyan dari daya.Bisa kidayar yawan mutanen da aka yi a karshen shekarar bara,an ce mutanen lardin sun kai miliyan 98.69,daga cikinsu miliyan 93.6 mazaunan dindindin na lardin. Bisa kididdigar da hukumar kidaya jama'a ta yi,an ce mutane miliyan 1.11 aka haife su a shekarar bara,mutanen da suka riga mu gidan gaskiya sun kai dubu 620.yawan mutanen da ake haifa a shekara ya kai kashi 11.26 cikin dubu,yawan mutanen da suka mutu ya kai 6.32 daga cikin dubu a shekarar bara.ainihin karin yawan mutane a shekara ya kai 4.94 cikin dubu.

Wani yaro ya sa maganin barci a cikin ruwan sha na ubansa. Wani mutum mai yawan shekaru arba'in da ake kiransa Shen yana da da a babban makarantar sakandare wanda ya ke so shiga yanar internet a birnin Zhengzho,babban birni na lardin Henan.wata rana da yamma ya sa maganin sa barci a cikin ruwan sha na ubansa duk domin ya samu damar shiga yanar internet. Da ubansa ya gane makircinsa sai ya yi kokarin kama shi. Da masu gadi na unguwan dake yin sintiri a kan hanyar Huayuan da karfe biyu da minti sha biyar na ranar talata sun ga abin da ya faru sun kare yaron daga ubansa. Daga baya yaron ya amsa laifin da ya aikata,ya ce kowace rana da yamma kafin ubansa ya sha ti ya kan sa maganin sa barci a cikin kwafin ti,da ubansa ya sha ti mai maganin sai ya yi barci sosai,shi ma ya samu damar shiga yanar internet ya yi wasa har daddare.Uban yaron ba ya yarda dansa ya yi wasa a yanar internet bayan karfe sha biyu na dare,Uwarta tana aikin dare.ba ta da damar kula da shi.

Bayan da ya gudu daga gidan wakafi ya sake komawa.An sami wani mutum mai suna Feng Junqiang wanda ya gudu daga gidan wakafi yau da shekaru 22 da suka shige yanzu ya mika kansa ga 'yan sanda ya sake shiga gidan wakafi,wannan abu ya faru ne a birnin Liuzhou na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta.Mai laifin ya koma gidan wakafi ne saboda ya jin labarin cewa yanayin gidan wakafi ya kara kyautata kwarai da gaske. Aka yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan wakafi,ya gudu a shekara ta 1985 saboda ya gaza yin hakuri da zama mai wuya a gidan.Ga shi yanzu ya shiga gidan wakafi, ya samu damar ziyarar kasuwa da shiga gasar kwakwalwa da kuma wasanni bayan da ya yi aiki a gidan wakafi.Wannan mutum na farko ne da yake da radin koma gidan wakafi bayan ya gudu a birnin nan.

Tsuntsu mai surutu ya zama matsala ga mai shi.Wani aku wanda ya iya magana da turanci da Putonghua da kuma Cantonese ya zama tauraro mai jawo hankulan mazaunan Yinghao a unguwar Haizhu ta birnin Guangzhou na kasar Sin.Wannan aku mai farin gashi da ake kiransa Jixiang ya iya yin lilo da sauran wasanni,shi ya sa mazaunan unguwa suna kaunarsa. Mai tsuntsun Xu yana kiwon aku shekara da shekaru,ya ce shi ma bai san daga ina akunsa ya samu irin kwarewa ba,ya kuma ce bai taba koya masa irin wannan fasaha ba. Tsuntsun Jixiang yana so ya jawo hankulan masu ziyara kuma ya yi farin ciki sosai yayinda ake kallonsa.Mai tsuntsun ya ce babbar illa ga akun nan ita ce ya yi surutu banza fiye da kima.(Ali)