Kwanan nan, gamayyar kasa da kasa na ci gaba da nuna jaje tare da samar da taimako ga yankunan da girgizar kasa ya shafa a kasar Sin.
Ministan harkokin waje na kasar Angola, Joao Bernardo de Miranda da ministan harkokin wajen jamhuriyar Trinidad da Tobago, Paula Gopee-Scoon, da ministan harkokin waje na kasar New Zealand, Winston Peters, da babban sakataren kungiyar NATO, Jaap de Hoop Scheffer, bi da bi ne suka nuna jaje ga bangaren Sin.
Ban da wannan kuma, gwamnatin Fiji ta bayar da kudin taimako da yawansu ya kai kimanin dalar Amurka dubu 16.6 ga kasar Sin. Sa'an nan, gwamnatin Uruguay ta bayar da na'urorin tace ruwa da darajarsu ta kai dalar Amurka dubu 100 ga kasar Sin. Har wa yau kuma, gwamnatin Poland ta yanke shawarar bayar da tantuna 160 ga kasar Sin, a yayin da gwamnatin Girika ta samar wa kasar Sin kayayyakin agaji da nauyinsu ya kai ton 5, ciki har da tantuna 100 da magunguna da na'urorin likita.
Bayan haka, ma'aikatar tsaron Jamus ta bayar da kayayyakin agaji da darajarsu ta kai kudin Euro miliyan 3 ga kasar Sin, ciki har da tantuna 80 da dai sauran na'urori.(Lubabatu)
|