|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-06-04 20:46:36
|
 |
Kasar Sin na son kara hada gwiwa tare da sauran kasashe a fannin yin rigakafin bala'u, da ba da agaji
cri
A gun wani taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a yau 4 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Son na son cigaba da gudanar da hadin gwiwa tare da sauran kasashe a fannin yin rigakafin bala'u, da ba da agaji.
Bayan faruwar babbar gigizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, kungiyoyin ba da agaji na gaggawa daga kasashen Japan, da Rasha, da Korea ta kudu, da kuma Singapore, sun halarci ayyukan ba da agaji, bayan haka kuma kungiyoyin likitanci 9 daga kasashen da abin ya shafa da kungiyoyin kasashen duniya, sun halarci ayyukan jiyya. Mr. Qin Gang ya ce, kasar Sin ta yi godiya sosai kan wannan.
Mr. Zhang Kening, shugaban sashen kula da harkokin duniya na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ya bayyana cewa, a cikin yunkurin sake raya lardin Sichuan bayan girgizar kasa, kasar Sin za ta cigaba da nuna ra'ayin bude kofa, don maraba da taimako da goyon baya daga kasashen dubiya, bisa bukatar da yankuna masu fama da bala'in ke yi. (Bilkisu)
|
|
|