Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-04 19:40:51    
Ma'aikatar kiyaye muhalli ta Sin ta fito da fasahohi iri 14 don bada jagoranci ga daidaita matsalar muhalli cikin gaggawa a wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa

cri

An labarta cewa, kawo yanzu dai, ma'aikatar kiyaye muhalli ta kasar Sin ta rigaya ta fito da fasahohi iri 14 da kuma sauran daftarai domin bada jagoranci daga dukka fannoni ga daidai matsalar muhalli cikin gaggawa a wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa yayin da ake yaki da bala'in da yin ceto.

An bayyana cewa, bayan aukuwar bala'in a ranar 12 ga watan jiya, tun farkon farko ne ma'aikatar kiyaye muhalli ta bayar da wata sanarwa kan rigakafi da shawo kan bala'un gurbata muhalli biye da bala'in girgizar kasa ; A lokaci guda, ma'aikatar ta kaddamar da ' Shirin ko-ta-kwana na gwamnatin kasa kan daidaita matsalar gurbata muhalli cikin gagauta' da zummar bada tabbaci ga samun kyakkyawan tsaron muhalli na wuraren da bala'in ya shafa.

Ban da wannan kuma, kwanan baya dai, gwamnatin kasar Sin ta riga ta soma gudanar da 'Ayyukan tantance tsaron muhalli na yankin Wenchuan bayan bala'in girgizar kasa mafi muni da kuma matakan da za a dauka don tinkarar lamarin'. Hakan ya kasance wani muhimmin abun dogaro ne a fannin kimiyya da fasaha ga sassan kiyaye muhalli wajen yanke shawarar shiga cikin yunkurin sake gina yankuna bayan bala'in. (Sani Wang)