Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 21:15:17    
Firaministan Sin ya shirya ayyukan farfado da aikin kawo albarka a wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa

cri

An labarta cewa, firaministan kasar Sin kuma babban mai bada jagoranci ga aikin yaki da bala'in girgizar kasa da yin ceto Mr. Wen Jiabao, yau Talata ya shugabanci zama na 16 na taron majalisar gudanarwar kasar, inda ya shirya ayyukan farfado da aikin kawo albarka a wuraren da bala'in ya shafa da kuma tattaunawa kan " Daftarin ayyuka na gwamnatin kasa kan sake gina yankuna bayan bala'in a Wenchuan".

Taron ya nuna cewa, ya kamata a dora muhimmanci kan farfado da aikin kawo albarka yayin da ake tsugunar da jama'ar da bala'in ya galabaitar da su; Sa'annan a yi aiki da kyau wajen gudanar da ayyukan noma da kuma farfado da aikin kawo albarkar masana'antu, da gagauta gyaran manyan gine-gine da kuma aikin saye da sayarwa a wuraren da bala'in ya shafa.

Kazalika, taron ya jaddada cewa, kamata ya yi a mayar da mutane a gaban komai yayin da ake yin wadannan ayyuka. ( Sani Wang)