Kwanakin nan, Sinawa a ketare da ke kasashen Indonesia da Cambodian da Jamus da New Zealand sun ci gaba da daukar matakai daban daban don bayar da kudin karo-karo ga yankunan da aka samu girgizar kasa a lardin Sichuan.
Ran 2 ga watan Yuni, shugaban babbar kungiyar Sinawa a lardin Sumatra da ke arewacin kasar Indonesia kuma jami'in kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta wurin Huang Yinkua da wakilan jaridun Sinancin da ke wurin sun je ofishin jakadancin Sin da ke kasar Indonesia, kuma sun isar da kudin karo-karo da yawansa ya kai miliyan 3.38 ga ofishin jakadancin Sin, don tallafa wa yankunan da aka samu girgizar kasa a lardin Sichuan a kasar Sin.
Ran 31 ga watan Mayu da yamma, shugaban kungiyar kasuwanci ta Taiwan da ke kasar Cambodian Jiang Yongxing ya jagoranci mambobinta, ya bayar da kudin ceton mutane da yawansa ya kai dalar Amurka dubu 32 ga ofishin jakadancin Sin da ke kasar Cambodian.(Bako)
|