|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-06-02 17:17:30
|
Mutane 69019 sun rasa rayukansu a sakamakon babbar girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan
cri
Yau 2 ga wata da yamma, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya sanar da cewa, ya zuwa ranar 2 ga wata da karfe 12, mutane 69019 sun rasa rayukansu a sakamakon babban girgizar kasa da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.
Bayan haka kuma, ya zuwa ranar 2 ga wata da karfe 12, a sanadiyar babbar girgizar kasar, mutane 373573 sun ji rauni, yayin da mutane 18627 suka bace.
Ya zuwa ranar 2 ga wata da karfe 12, kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyakin da ke da darajar kudin Sin RMB biliyan 41.7 daga bangarori daban daban na gida da na waje, kuma an riga an bayar da taimakon kudi da na kayayyaki da ke da darajar kudin Sin RMB sama da biliyan 11.5 ga yankuna masu fama da bala'in. (Bilkisu)
|
|
|