Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 14:16:57    
Hukumar noma da ta ban ruwa ta yankunan da aka samu bala'in girgizar kasa da mutanen da suke shan wahalar bala'in sun kaddamar da aikin taimakon kansu cikin himma

cri
Kwanakin nan, hukumar noma da ta ban ruwa ta yankunan da aka samu bala'in girgizar kasa da mutanen da suke shan wahalar bala'in sun kaddamar da aikin taimakon kansu cikin himma.

Game da halin da ake ciki na karancin ruwa a yankunan da aka samu girgizar kasa a lardin Sichuan, an canja noma wasu amfanin gona da ake nomawa a cikin ruwa da amfanin gona da ake nomawa a yankuna masu fari, ma'aikatar noma ta tuntuba kuma ta yi shawarwari tare da kamfanonin iri fiye da 20 na kasar, wajen gaggauta daukar irin masara mai aure 40 da yawansu ya kai kilogiram fiye da miliyan 10 zuwa yankunan da aka samu bala'in girgizar kasa, haka kuma an kai irin kayan lambu na kabeji da karas da wake da yawansu ya kai kilogiram dubu 500 zuwa wurin.

Ya zuwa yanzu, ma'aikatar noma ta yankunan da aka samu bala'in girgizar kasa, gaba daya dai sun ba da jagoranci ga kungoyoyi masu ba da taimako da yawansu ya kai 5500 wajen taimaka wa manoma girben amfanin gona da yin shuke-shuke. Wani jami'in ma'aikatar noma ta lardin Sichuan ya bayyana cewa, ya zuwa ran 24 ga watan Mayu, lardin Sichuan ya riga ya girbe alkama da yawansu ya kai kashi 92 cikin kashi 100, an shiga lokaci na karshe wajen girben irin ganyaye masu ba da mai da yawansu ya kai eka dubu 900, haka kuma an riga an noma shimkafa da yawanta ya kai kashi 78 cikin kashi 100. Ana kyautata zaton cewa kafin ran 5 ga watan Yuni, za a girbe dukkan amfanin gona daga dukkan fannoni.

Babbar girgizar kasa ta kawo mummunan cikas ga aikin ban ruwa na yankunan lardunan Sichuan da Chongqing da Gansu da Shanxi na kasar Sin. Bayan da ma'aikatar ruwa ta gaggauta yin musu gyare-gyare, ya zuwa yanzu, lardunan daban daban na yankunan da aka samu girgizar kasa a kasar Sin da yawansu ya kai kashi 80 cikin kashi 100 sun farfado da samar da ruwa.(Bako)