A kwanakin baya, Mr. Jia Kang jagoran hukumar nazarin kimiyyar harkokin kudi ta ma'aikatar kudi ta kasar Sin ya ce, ya kamata a tara kudi daga dukkan sassan kasar Sin ta hanyoyi dabam daban domin sake gina gidaje a wuraren da ke fama da bala'in girgizar kasa.
Game da hasarar da aka samu a sakamakon bala'in, har zuwa yanzu, ba a sanar da sakamakon kididdiga ba. Amma mai yiyuwa ne, yawan harasa zai kai RMB Yuan biliyan darurruka. Mr. Jia Kang ya ce, saboda matsanancin hasara, kudin da gwamnatin ta gabata ba za zai biyan bukata ba, ya kamata a tara kudi daga dukkan sassan kasar Sin ta hanyoyi dabam daban domin sake gina gidaje.
Mr. Jia Kang ya yi nuni da cewa, ba kamar bala'in girgizar kasa da ya auku a birnin Tangshan kafin shekaru 32 ba, a lokacin can, kasar Sin tana cikin halin tsararren tattalin arziki, gwamnati ta ba da dukkan kudin sake gina gidaje. Yanzu kasar Sin ta riga ta shiga tsarin tattalin arziki na kasuwanci, yayin da gwamnati ke samar da kudin sake gina gidaje, ya kamata a tara kudi ta hanyoyi dabam daban.
|