Bayan da mummunan bala'in girgizar kasa ya fadawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kungiyoyin jam'iyyar kwaminis na matakai daban-daban, da mahukunta 'yan jam'iyyar da dama sun maida moriyar jama'a a gaban kome, kuma sun bayar da babbar gudummowa ga ayyukan yaki da bala'in da ceton mutane cikin nasara. Sabili da haka ne, Jaridar People's Daily ta kasar Sin ta bayar da wani muhimmin bayani a shekaranjiya wato ranar 31 ga watan Mayu mai lakabi haka, "Kasancewa tare da jama'a har abada----Ga 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadanda suke aiki tukuru wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane".
Bayanin ya yi nuni da cewar, bayan da bala'in girgizar kasa ya auku, sakatare-janar Hu Jintao ya bada muhimmin jagoranci cewar kamata ya yi a ceci wadanda suka ji rauni ba tare da bata lokaci ba, domin bada tabbaci ga zaman lafiyar mutanen da bala'in ya ritsa da su. Haka kuma, awoyi biyu kawai bayan aukuwar girgizar kasa, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya je yankunan dake fama da bala'in, a wani yunkurin jagorantar ayyukan yaki da bala'in da ceton mutane. Kazalika kuma, zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira taro a wannan rana dare, domin tsara shirye-shiryen ayyukan yaki da bala'in da ceton mutane, haka kuma sashen tsara shirye-shirye na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bukaci kwamitocin jam'iyyar kwaminis na matakai daban-daban, da mahukunta 'yan jam'iyyar da su taka rawar a-zo-a-gani wajen bada jagoranci. Dukkan wadannan al'amura sun shaida irin aniyar da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kudura na yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane, wato bala'in shi ne umurni! Lokaci shi ne rayukan mutane! Rayukan mutane sun fi kome muhimmanci!
Bayanin ya kuma kara da cewar, a yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su, kungiyoyin jam'iyyar kwaminis na kananan hukumomi na lardin Sichuan sun kafa kungiyoyin ceton mutane na 'yan jam'iyyar da yawansu ya kai dubu 18, akwai kuma mahukunta 'yan jam'iyyar kwaminis sama da miliyan 1.76 wadanda suke aiki tukuru a yankunan dake fama da bala'in. Kungiyoyin jam'iyyar kwaminis na matakai daban-daban, da 'yan jam'iyyar suna aiki ba ji ba gani wajen yaki da bala'in da ceton mutane. Daga wajensu, muna iya ganin babban nauyin dake bisa wuyan 'yan jam'iyyar kwaminis, wato maida zaman lafiyar jama'a a gaban kome.
Bayanin ya kuma jaddada cewar, irin halayyar da 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suke nunawa yayin da suke kokarin yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane babbar halayya ce ta duk al'ummar kasar Sin. Muna da imanin cewa, ko shakka babu, al'ummar kasar Sin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za su cimma galaba kan mummunan bala'in girgizar kasa!(Murtala)
|