Bayan da girgizar kasa mai tsanani ta afkawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan a ran 12 ga watan Mayu da ya wuce, a wani matsuguni mai suna "gida mai kauna" da ke birnin Chengdu, an tsugunar da jama'a sama da 700 da girgizar kasar ta galabaitar da su, wadanda suka zo daga garuruwan Qingchuan da Wenchuan da Deyang da Dujiangyan dai sauransu, ciki kuwa har da yara sama da 100. Bisa kauna da kulawa da bangarori daban daban suka nuna musu ne, yaran suka shiga ranar yara ta duniya.
Tun daga ran 26 ga watan Mayu ne, aka farfado da darrusa ga yaran da ke wannan matsuguni. Domin taya su murnar ranar yara, matsugunin ya ba su kyaututtuka iri daban daban. Bayan haka, matsugunin ya shirya musu bukukuwa. A ranar yara, ta wayar tarho ne, yaran da ke matsugunin za su iya yin hira da shahararren dan wasan kwallon kwando na kasar Sin, wato Yao Ming, wanda yanzu haka ke kasar Amurka.(Lubabatu)
|